Dole a Samu Shugaba Cikin Kowace Tafiya !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @ Shafi Domin Kai Da Al'ummar ka

YAKAN ZAMA SHAIDANI KO KUMA MAI SHIRYARWA

Tunda Annabi (S.A.W.W)yayi umarni da cewa a sami shugaba cikin kowacce tafiya da ta faro daga kan mutum biyu zuwa sama, to, dole ne a samu , sai dai ya kasance ko Shaidani mai halakarwa ko kuma mai shiryarwa.

Shi kuma wannan shugaba zai iya zama na wucin-gadi (temporary)wanda zai iya gabatar da wasu al'amra a madadin shugaba (permanent)wanda ake samun shiriya ko kuma bata daga gare shi.

Za ku iya fahintar haka ta hanyar fayyacewar da Manzon Allah (S.A.W.W)yayi mana da cewa Shaidan yakan samar da wani mataimakinsa daga Aljanu ko kuma mutane wadanda za suyi masa aiki wajen halakar da bayin Allah masu biyayya ga koyarwar Manzo (S.A.W.W).

Yayin da Annabi (S.A.W.W)zai bar duniya sai da ya halifantar da wanda zai shiryar da al'umma kan tafarkinsa kamar yadda ya bar al'ummar.

Ko da a wannan zamani mun san Imam Mahdi (A.F)shine Limamin qarshe wanda muke jiransa don ceto al'umma daga halin da suke ciki, sai dai a daidai wannan lokaci da yake cikin Ghaiba ba kowa ne ke samun umarninsa ko kuma zantukansa ba sai ta hanyar wasu bayin Allah nagartartu.

Sayyid Zakzaky (H)shine jagora 1
wanda babu shakku ko kuskure tare da shi cikin al'amarinsa, sai dai a halin yanzu ba ya cikin mu a bayyane, sannan bai yi umarni  da cewa ga mutum 1 rak wanda daga gare shi za mu riga ji da daukar komai ba, amma dai yakan umartanmu da cewa mu kasance kan nizamin da ya barmu a kansa.

Saboda haka duk wani yunquri da almajiransa (H)za suyi matuqar sun kai mutum 2 zuwa sama, to, akwai wanda ya bada umarni ko kuma shawarin aikata wannan aiki.

Idan kuwa ya kasance haka, to, wannan mutum shine jagoranka akan wannan aiki komai kyansa kuma komai muninsa.

Saboda haka wanda ka ji yana magana da nufin sukar wani, to, haqiqa ba don Allah yake yin wannan abinda yake yi ba.

ALLAH YA TABBATAR DAMU KAN GASKIYA.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 9th Dec, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post