-Wani Malamin Kiristoci yazo wajen Imam Musa Al-Kazeem (As) yana Iƙirarin yana da ilimi mai zurfi akan Attauta da Injeela.
-Imam ya tambayeshi sunan Mahaifiyar Sayyada Maryam da kuma waje, lokaci, da kwanan watan haihuwar Annanbi Isah (As), Malamin Kristoci yace bai sani ba.
-Imam (As) yace, "Zan sanar dakai akansu, Sunan mahaifiyar Sayyada maryam (S.a) a yaren Greek 'Martha' wanda yai daidai a larabci da 'Wahba'.
-Ganawar Annanbi isa ya faru ne a yammacin Juma'a. An aiko Mala'ika Jibreel zuwa ga Sayyada Maryam a wannan lokacin.
-Manzon Allah ya wajabta ranar tazam ranar Eidi, Musulmai su taru a wajen domin yin bauta.
-An haifi Annabi Isah ranar talata. an haifeshi ne a wajen kogin 'Yufiret'.
-Allah maɗaukakin sarki ya ni'imtar da manoma da falallarsa, manoma sunce an sami yalwar Dabino da Inibi.
-A wannan rana Maryam batai magana da kowa ba, loakcin da Sarki Qaidoos yaji haka, yasaka a kira masa mutane daga yarenta, ya basu umurni: Gaba ɗayanku kuje ku tambayi Maryam game da gaskiyar wannan haihuwa.
-Mutane suka tafi ga Sayyada Maryam suka ce, "Ya Maryam! kin aikata sabon abu! yake ƴar uwar Harun, babu ɗaƴa cikin mahifinki da mahaifiyarki da ya zama mai aikata aikin banza".
-Yakai Malami! Gayamin wannan wacce rana ce? Malamin yace, a Injeela ana kiranta da sabuwar Rana 'New day'.
-Imam (As) yace, "Ba rana ta musamman ba. Hakan yana nuna mutane sun nuna murɗiya ga abinda aka zo dashi na daga littafin Allah.
-Malamin yace, "Domin mu gasgata hakan kana da iilimin abinda ba m'a gani? Zan ƙalubalanceka da ka faɗa min sunan Mahaifiyata."
-Imam yace, " A yaren Syria ana kiranta 'Utgaliya' a Arabin kuma 'Maliha'. Sunan Kakanka kuma Unfoor mahaifinka kuma Abdul Masih.
-Wannan sunan ba daidai bane; yakamata yazam Abdullah sabida babu wanda zai iya zama bawan Masih (Jesus).
-Sunan Kakanka ta wajen Uwa shine Jibraeel. Shima ba daidai bane. Yakamata ya zama Abdur Rahman. Sabida ba'a yarda a sawa mutune sunan Mala'iku ba.
-Yanzun saurari labarin kashe Kakanka. "mutanen Syria ne suka zagaye mazauninsa (gudansa) suka kasheshi.
-Malamin Kristoci yace, "Yanzun gayamin, menene sunana? Imam yace, "Sunanka Abdul Saleeb, amma ba haka yakamata ya kasance, Abdullahi ne ya dace."
-Da Malamin ya gama jkn dukkan waɗannan zantukan yace, da yardar ya zama Musulmi.
Allahumma salli ala Muhammad wa ali Muhammad√√√√√
_____
Bιπ 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ