Dalilin Muslimtar Sayyadina Abubakar !!! (1)


Shekara (6) Shida Bayan Manzan ci.

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED 

Kamar yadda tarihi ya kawo cikin dukkan littafan muslimci shine, Sayyidinah Abubakar ya kasance aboki wajen Manzon Allah (S.A.W.W)tun daga halin quruciya har tafiyarsu Hijra zuwa Madinah suna tare kamar yadda Qur'ani ya kawo.

Amma sababin muslimtarsa shine, bayan aiko Manzon Allah (S.A.W.W) da shekara 6 yayi tafiya zuwa Sham don fataucinsa kamar yadda ya saba sai yayi mafarki cewa Rana da Wata sun sauko cikin dakinsa sai ya kama su ya lullube su da bargonsa.

Bayan farkawarsa daga bacci sai ya tafi wajen wani Rahibin malamin Nasara ya tambaye shi fassarar wannan mafarki. Sai Rahibin ya tambaye shi cewa shi mutumin ina ne kuma a wacce qabili yake? Bayan ya ba shi amsa sai malamin yace masa;

‘’ TO, WANI MUTUM ZAI FITO A ZAMANINKA ANA CE MASA MUHAMMADU DAGA CIKIN QABILAR BANU HASHIM, KA BI SHI SHINE ANNABIN QARSHEN ZAMANI. BA DON SHI BA DA ALLAH BAI HALICCI SAMMAI DA QASSAI BA, KUMA DA BAI HALICCI ADAM DA SAURAN MANZANNI BA, MUN SAMI KAMANNINSA CIKIN INJILA DA ZABURA KUMA NI MA NAYI IMANI DA SHI, SAI DAI NA BOYE SHINE CIKIN ZUCIYATA ‘’.

Duk da wannan fassara bata sa ya muslimta har sai da wata rana Annabi (S.A.W.W)yace masa;

‘’ YAA ABUBAKAR, KOWACCE RANA KANA ZUWA KA ZAUNA DANI AMMA BA ZA KA MUSLUMTA BA ?‘’

Sai Abubakar yace masa;‘’ Idan kai Annabi ne zai yi kyau ace ka nuna wata mu'ujiza da zan yarda da kai .‘’

Sai Manzon Allah (S.A.W.W)yace masa;

‘’ BAI ISHE KA MU'UJIZA BA ABINDA KA GANI CIKIN MAFARKINKA WANDA RAHIBIN NAN YA FASSARA MAKA ?‘’

Wannan ne yayi sanadin muslimtarsa.

Sayyidinah Abubakar ya muslimta yana da shekaru 43, domin Annabi (S.A.W.W)ya ba shi shekara 2.

Za mu cigaba insha Allah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

~ 1st December, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post