*Jagoran gaskiya* [sayyid zakzaky]
Shakhsiyyar mutum a ce shi wane ne, to lallai alal haqiqa shi ne shi.
Domin kuwa idan ka ga mutum, farkon ganinka da shi, yadda jikinsa ya
bayyana, kila da shi za ka auna ka ce shi kaza ne. Kamar alal misali ka
ce shi wannan mutumin fari ne ko baqi ne, dogo ne ko gajere ne, tsoho
ne ko yaro ne, ko abin da ya yi kama da haka nan. Amma in ka zauna da
shi ku ka saba, ku ka dade tare, to in ka gan shi, yanzu wani abu kake
kallo, dabi'unsa kake kallo tunda yanzu ka san shi.
Muqaddara wannan mutumin yana da kyawun halitta da hancinsa mai
kyau da gashinsa mai kyau, kuma mutum ne mai tsafta, rigunansa fes-fes. Amma da aka zauna da shi sai aka ga mai mugun hali ne. Bari mu ce
alal misali da aka zauna da shi sai aka gane cewa shi barawo ne, yana
Dauke-dauke. To ranar da ya zo fes-fes da kyakkyawan tufar nan tasa
yana gabatowa, a ranka wa kake ganin yana zuwa? Barawo kake gani!
Yanzu ka ga an fara kaffa-kaffa.
Ka ga a nan kyawunsa ya zama abin da Bahaushe ke ce wa kyawun dan
maciji. Saboda yanzu ba kuma kyawun kake gani ba, mummunar
dabi'arsa kake gani. Ka ga wannan ashe ya nuna maka dabi'a ita ce
mutum.
Na'am muna iya cewa sifa zahiran Allah ya yi wa mutum da ma ba shi
ya yi wa kansa ba, ko da shi kyakkyawa ne na halitta, wannan in ma da
wanda za a yaba wa a kan kyawunsa, sai a yaba wa Allah wanda ya yi
masa halitta. To amma wannan mummunar dabi'ar shi ya yi wa kansa,
ba Allah ya yi masa ba. Ka ga wannan shi ne shi a haqiqani ba halittarsa
ba. To kuma ka ga gobe qiyama ladar me za a ba shi, ko kuma laifin me
za a kama shi da shi, ko da me za a yi masa hisabi? Da dabi'arsa ko da
halittarsa? Da ma ita halitta Allah ne ya yi masa ita yadda ya so. Ka ga
ashe dabi'ar mutum shi ne shi!
*©Mahadi Tukur Almizan*
{TASIRIN DABI'U}