Da Mutuncin Buhari da Kimarsa duk ya Zubar da su a Zariya...!!!


WAJEN ZALUNCINDA YASA AKAYIMA SHEIKH ZAKZAKY (H) DA ALMAJIRANSA!

Za'a dinga tunaka da zaluncinda kafara a farkon mulkinda ka shekara 12 kana nemansa baka samu ba, amma lokacinda kasamu saiyazama duk fushin rashin samun mulkinda bakayi ba a wannan shekarun da bakin cikinda kayi duk saika zazzage su akan Jagoran addini, wanda yakema Allah hidima a tsawon rayuwarsa.
Kai kace Sheikh Zakzaky (H) ne yahana aba Buhari mulki tun lokacinda yake ta neman samunsa, sai mutum yayi mamakin wace irin gaba da kiyayya ce Buhari yakema Sheikh Zakzaky (H)? Wadda haryasa yayi masa wannan irin mugun Zaluncin? Kana hawa mulki maimakon kagode ma Allah da samun abinda kayi shekaru kana nema bakasamu ba, sai a wannan lokacin. Sai kuma kawai akaga akasin haka kakoma kana fada da abinda Allah (T) yake tsananin so da kauna (Addininsa) ina kai ina fada da Allah (T)!

Tunda wannan gwamnatin tayi wannan mugun bakin zaluncin, tundaga wannan lokacin Allah (T) yakwashe mata albarka duk abinda take fata yazama tarasa shi, baitil malin yazama kamar rariyar hannu duk abinda yazo saidai ya zurare. Kuma Insha'Allah sakamakon abinda zaizo nangaba yafi abinda ake akai a yanzu, sai anyi danasani kuma lokaci nanan zuwa wanda za'a gasgata zancennan.

Menene Sheikh Zakzaky (H) yayima Buhari ne yake tsananin nuna kiyayya dashi? Kiyayyar wannan mutum akan wannan bawan Allah ta tsananta takai intaha, amma kuma za'a girbi abinda aka aikata Insha'Allah.

Allah (T) katausaya mana da fitowar Jagoranmu Sheikh Zakzaky (H) Allah (T) kayi mana sakayya akan zaluncinda akayi mana, Allah (T) ka'amfanardamu.
~~~~~Abba Salisu~~~~~

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post