CIKAKKEN RAHOTO DAGA HARAMTACCIYAR KOTUN ZALINCI TA KADUNA

Yadda ta kasance game da Shari'arsu Malam Zakzaky (H) yau Alhamis daga babbar kotun kaduna

Dukkan bangarorin lauyoyinda ke cikin wannan shari'a sun iso kotu. Banganen lauyoyin gwamnati, lauyoyin DSS, Lauyoyin 'yan sanda da kuma na su Sayyid duk suna cikin kotu. Shigowar alkali kawai ake jira.

Yau Barista Haruna Magashi ne zai wakilci Femi Falana a wannan shari'ar. Ya yin da Bayero Dari ke jagorantar lauyoyin gwamnati. Alkali ya shigo,Bayan Alkali shigo, Lauyan gwamnati ya shaida wa kotu cewa an sanya ranar yau ne don ci gaba da wannan shari'ar.

Amma lauyan Sayyid ya nemi da a dage zaman yau a cewarsa tun da su Sayyid (H) suka dawo daga India ba a baiwa lauyoyinsa damar ganinsa ba. Saboda haka suna neman kotu da ta sanya DSS su bar su ga Sayyid Zakzaky (H)

Lauyan gwamnati ya musanta wannan maganar, ya ce akwai dangantaka mai kyau tsakanin DSS da lauyoyin su Malam (H). Ya ce ko jira Barista Sadau Garba ya ga su Malam (H). Don haka ya nemi kotu da ta mayar da su Malam gidan yarin Kaduna (Central Prison Kaduna). Ya ce hakan zai baiwa kowa damar ganin su Malam (H) duk lokacin da yake so.

Kotu ta bada umarnin mayar da su Malam (H) gidan Yarin Kaduna yau. Sannan ta ba da umarnin a bar lauyoyin su Malam su gansu duk lokacin da suke so.
An dage zaman sai ranar 06/02/2020

05/01/2019

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post