TARE DA MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATE
ban garen yan uwa sisters mahalarta bukin maulidin |
Wani ban gare na Yan uwa brothers du awajen mauluddin |
Sha'iran harkar musulunci ayayin da suke rere baitoco |
Mlm Muhammad kabir imam wakilin Yan uwa na garin malumfashi yayin daya ke jawabin godiya |
Sheihk sharif khidir kano yayin daya ke jawabi wajen bikin mauluddin fiyayyan halitta annabi (a.s.w.w)agarin mlf |
An gudanar da gaggarumin bikin mazalasin mauluddin fiyayyan halitta annabi Muhammad (a.s.w.w) a kofar gidan Dan uwa sulaiman garba gangarawa gandu malumfashi
Anfara gudanar da gaggarumin bikin mauluddin tun misalin karfe 5:00pm na ranar lahadin data gabata Wanda alhaji mustapha umar baba gadon kaya ya faru bude taro da majalasi bayan sallar isha'i kuma aka ci gaba daga inda aka tsaya
Wanda babban baqon mu yayi kwalakwalan jawabai ya fadi irin yanda kafiran makka suka quntatawa manzon Allah (a.s.w.w) da kuma yanda wasu daga cikin sahabbai sukai tayi Mai zagon kasa har zuwa wafatin shi
Babban ya fadi irin yadda aketa so aga bayan Kiran manzon Allah (a.s.w w) tun yana karamin shi har zuwa wannan lokacin kafirai da azzaluman bayi suna Nan da qudirin su na ganin sun dishe wannan haske na fiyayyan halitta annabi Muhammad (a.s.w w)
Angudanar da majalasin mauluddin ne don nuna kauna da samuwar fiyayyan halitta annabi Muhammad (a.s.w.w)kuma ya samu vhalartar babban shehin malamin sheihk sharif khedir daga kano
Tare da sheihk sharif sanusi sarki duk cikar su daga kano
Daga karshe malam Muhammad kabir imam malumfashi yayi masu jawabin godiya sannan yasake miqa abun magana ga babban baqon ya rufe taro
Fatan Allah ya karbi idar mu ya kuma Mai Mai ta Mana na shekara Mai zuwa cikin koshin lafiya da yalwar arzuki
MDN BARA'A MALUMFASHI
Tags:
Labaran Duniya