Ita dabi'a a jikin mutum take cikin rai wacce take tasirantuwa ga ma'abocinta, mai kyau ce ko mummuna, sai dai wani lokaci akan iya canza ta ta hanyar samun kyakkyawar tarbiya.
Fadin Allah (T)ne cewa yana fitar da rayayye daga matacce, kuma yakan fitar da matacce daga rayayye. Kowa zai iya fahintar haka matuqar yana bibiyar yanayin tarbiyyar 'ya'yan gidaje mabambanta, domin zai iya ganin mai kyakkyawar tarbiyya ta fito daga iyaye marar sa tarbiyys, wani lokaci kuma iyayen ne masu tarbiyya, 'ya'yansu kuma babu ita.
Wannan dai shimfida ce nayi don na nuna mana cewa ko da ka ga sister da rashin tarbiyya, to, ka sani cikin amawa ma haka ake samu. Kuma ko kaga tarbiyyah cikin amawa haka ma za ka gani cikin sistoci.
Sai dai kuna sakamakon tarbiyyar harka islamiyyah za kaga sistoci sun sha bamban da matan amawa, ko da kuwa sun yi tarayyah da su cikin wasu munanan dabi'u.
Sistoci sun kebanta ta wajen shiga irin wacce muslimci ya yarda da ita, wato ta fuskacin sanya Hijabi gwargwadon koyarwar muslimci. Duk wani munin hali da kake da shi na dabi'a in har ka kalli shigar da take yi zai faranta maka rai, domin abinda zai tuno maka shine shigar matan Sahabbai yayin saukowar ayar Hijabi.
Sister ita wacce za ka gamsu da fitarta ba tare da tunanin wani abu daga sharrin shaidan zai shafe ta ba, domin shigarta na tsorata shaidanin mutum dana Aljan daga shafarta.
Ita kuwa ba'amiya ko da tana da tarbiyya sai ka raina mata wajen shigar suturar ta, domin za ta iya boye maka guraran da suka halatta gare ka, kuma su bayyanar maka guraren da ganin su ya zama haramun gare ka.
Kenan matuqar mace za tayi haka ta tashi daga matsayin mai tarbiyyar muslimci komai kyawawan dabi'unta. Saboda haka sanyin zuciya ta nutsuwarta shine kaga Allah ya mallaka maka sister a matsayin abokiyar zama.
TO SEE HER DRESS AND FEEL JOY IN YOUR HEART !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-0
Tags:
Tunatarwa