...Shafi Domin Kai da Al'ummar ka
www.maasumah.com.ng
Duk da cewa mutane sun jirkita rarihi sun murgada shi inda suka so don su boye gaskiyar abinda ya faru a tarihin muslimci, amma hakan bai hana wasu fito da gaskiyar maganar ba cikin rubuce-rubucensu.
Daga cikin abinda aka boye na gaskiya akwai batun mafarkin Manzon Allah (S.A.W.W) wanda yayi har Allah ya sanya shi futina cikin mutane.
Sun murguda shi cewa wai a daren da Annabi (S) yayi Isra'i ne yaga abinda ya gani a bayyane (reality) ba wai a cikin mafarki. Kuma wai bishiyar da aka tsine mata cikin Qur'ani ita ce bishiyar ZAQQUN.
Ta yadda za a gane maganar cewa qarya ce shine, Allah (T) ya ambaci abinda Annabi (S) ya gani cikin mafarki ne (RU'UYA) ba wai a farke ba.
Sannan Ibn Jarir 'Dabari yace;
An bani labari daga Muhammad Bn Hassan Bn Zabaalata ya bani labari, Abdul-Mumini Bn Abbas Bn Sahal Bn Sa'ad ya bamu labari, babana ya bani labari daga kakana yace;
" Manzon Allah (S.A.W.W) ya ga iyalan gidan wane (BANU UMAYYAH) suna hawa kan Mimbari kamar yadda Birrai ke hawa (sama), sai hakan ya bata masa rai, tun daga nan bai qara yin dariya ba (don baqin ciki) har ya rasu."
Yace, daga nan sai Allah ya saukar da;
" BA MU SANYA (wannan) MAFARKIN DA MUKA NUNA MAKA BA FACE FITINA GA MUTANE, DA KUMA BISHIYAR NAN DA AKA TSINE MATA CIKIN ALQUR'ANI."
(Isra'i, aya ta 60)
Tafsir na 'Dabari, J:15, Sh:77).
Dan Allah akwai babbar fitinar da Annabi (S.A.W.W) ya bari a bayansa kamar BANU UMAYYAH???
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470-08137925034