MALAM BAHAUSHE ..KENAN....WANDA DUKKAN YARURRUKA DA KABILU KE YI WA KALLON HADARIN KAJI SABODA WASU DABI'U NASA NA RASHIN KISHI DA TSARI DA HADIN KAI...
A Kudu BAHAUSHE NADA SUNAYE DA YAWA DA AKE KIRAN SA DASU ..WADANDA BASA NUNA KIMA KO GIRMAMA WA ZUWA GARE SA ..
SUNAYEN SUN HADA DA ..MOLA...ABOKI.
..AWUSA.. ALMAJIRI MAI SUYA ...OMO GAMBARI..ONYI GBU.. ...BOKO HARAMIST....DA SAURAN SU.
..
Fulani su kirashi KADO...Buzaye su kirashiI ...ATAIFUN...
...
Inkaje Benue ankiransa ORIKE a Barno suna kiransa APUNO wasu suce masa KIRDI..
Ban san Mai sauran Kabilun AREWA Ke kiran sa ba
..
Amma daiI Dukkan su suna kaskantar da DARAJAR SA ne ba GIRMAMAWA BA.
...
KAFIN MU CI GABA DA WANNAN BAHASI
BARI MUJI MAI WANI MANAZARCI YA RUBUTA..
..
..
Ramin Kura..
..
..
Babu wata jinsi wadda ta zama ana kashe jinsinta tana murna wadda tafi hausa.
Duk duniya babu wasu jinsin al'umma dake sace kayan wadanda ake kashewa kamar hausawa.
Babu wadda zaka ga ana kashe 'yan-uwansu suna dariya kamar hausawa.
Babu wadda zaka ga an kashe mamatansu suna sace kayansu kamar hausawa.
Hatta Dabbobi idan suka ga ana kashe 'yan-uwansu, to ba zama suke yi ba, guduwa suke. Saboda sun san idan aka gama da sauran kansu za a dawo, amma abin mamaki da rashin hankali, Bahaushe ana kashe 'yan-uwansa hausawa shi kuma zaka ga sai murna yake.
BANSA MUSULUNCI BA, MUSULUNCI DABAN HAUSA DABAN, MASU MURNA DA KASHE MUSULMI BA KOYARWAR MUSULUNCI SUKE AMFANI DA SHI BA, MUSULUNCI YA HANA KASHE KAFIRI BARE KUMA MUSULMI.
Allah wadaran mutanen da Dabbobi suka fisu tunani da hangen nesa, wai kuma a ciki harda wasu da ake kira Malamai...
....
.. TUNA BAYA: Wakar Sa’adu Zungur Mai Taken Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?
....
“Matukar a arewa da karuwai,
‘Yan daudu da su da Magajiya.
....
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
....
Matukar ’ya’yan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
....
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
...
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai taryonsu da dukiya.
...
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
...
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
....
Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,
Malaman karya ’yan damfara.
...
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
....
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
....
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
.....
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
.....
Wagga al’umma mai za ta yo,
A cikin zarafofin duniya.
....
Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya.
....
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.
.....
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
.....
Gaskiya ba ta neman ado,
Ko na zakin muryar zabiya.
.....
Karya ce mai launi bakwai,
Ga fari da baki ga rawaya.
....
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
....
Marigayi Sa’adu Zungur a cikin waken sa mai suna “Arewa