Ba dadun Zagi Babu Kyau ba da Sai Nace Ko Uban Ka Yayi Kadam Ya Rusa Shi'a..!


Cewar Sayyid Zakzaky (H)
Daga zauren jawaban Sayyid Zakzaky(H)
.
Idan kace wani ne ya kirkiri Shi'a, to makirkirin ta shine Allah , madashin ta shine annabi ,to ina kai ina rusa abinda Annabi ya dasa ai kayi kadan, ba dadun zagi babu kyau ba da sai nace ko uban ka yayi kadan ya rusa shi'a,

Ina nufin uban sa Fir'auna da namarudu iyayen gidan sa na baya , namarudu uban sa ko kakan sa da ya jefa Annabi Ibrahim a wuta shikenan komai ya kare ? sai aka nemi Ibrahim aka rasa ? sai addini ya kare ? to fir'auna kuma fa da yayi abubuwan da yayi ya dinga yanka 'ya 'yan bani isra'ila sai aka nemi musa aka rasa ? sai addini ya bace ?? Tooo kaga uban ka kenan to ballanta kai karamin alhaki addini kam sai dai ka mutu da bakin ciki amman bazai kasu ba .

Amman kamar yanda nace zan musu gargadi nasan baji zasu yi ba ,abinda da ban mamaki ace mutun kullun shi bashi da wani tunani sai shi wai kullun zaiyi kisa ne , zaka kashe mutane kai mene? Wai ka rayu wai shi yana ganin duk abinda ya zama barazana gareshi ya kawar dashi wai sai ya rayu abinsa to wa kake ganin yake rayuwa ,
Yanzu lura da wadannan wanda suka wuce wadanda sukai kashe kashe su ka wuce dauki dolo da bindiga misili wani jibgegen kato da ainihin ya bude wuta da rana tsaka yai kashe kashe yai kashe kashe to wa yaje ya kashe shi ai nihin ance gidan da yake kwana sai ka wuce kofa goma sha biyu kafin ka shiga gidan to amman mala'iku basu bude ko daya ba basu kuma bude silin ma amma sai ga kato rigijaaa , ina yake ? To ina mulkin da yake son karewa ? Ina rayuwar tasa da yake so ? Bashiii to kuma nan kan idon ku kwanan nan wani ya gama murmurewa , ya murmuren ya murmuren ya murmure to don Allah in ba kaima kana son ka murmure ne ba memene naka na zumudin zakayi kisa ? Kai kisa ka rayu kaci mene kaima ba rayuwa zakayi ba amman nasan bakwa Jin magana ku kullun tunanin ku zakuyi kisa ne kuna kuma da ubangijin ku iblis yana ingiza ku yana nuna muku mafita gareku shine kuyi kisa ga duk wanda yake ingiza ku .

*Wannan wani yanki ne na jawabin da Sayyid Zakzaky(H) yayi a ranar Yaumus Shuhada 2010*

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post