Duniya baki daya baza ta mance da wannan rana ba.
Hakika wannan rana ce da Musulmai a Nigeria suka tsinci kansu a cikin wani mummunan yanayi na ta'asa ta rashin imani Wandas sojojin Nigeria suka yi akan Musulmai yan uwa almajiran sayyed
zakzaky H a garin zariya.
Hakika an zubar da jini na bayin Allah Masu yawan gaske Wanda ciki harda,
Yayan maulana Sheik ZAKZAKY H guda hudu.
Sai yayar Sheik ZAKZAKY H da aka kona da ranta.
Sheiks turi, Sheik Mustapha, Sheik muktar sahabi, Dr Mustapha,
Hamza yawuri, Hafiz Dauda, da jiga jigan yan uwa Masu yawa, wasu
an tabbatar da shahadar su, wasu kuma ana tsammanin haka.
Masu cikakken Imani sama da rai dubu da alkaluma suka nuna
sunyi shahada.
A ranar aka rushe Hussainiyya, Darur Rahma, Fudiyya Centre, Gidan
Sayyid ZAKZAKY H, da kuma gidan ummul mujaddadi umma Hari.
Ya Salam.
An harbi maulana Sheik Ibrahim zakzaky H harbi mai yawa, haka ma
ummul Shuhada malama Zinatuddin,,, tare da dukkan wadanda suke
tare da su. Wasu sun tsira da rai wasu kuwa sunyi shahada gabans su Sayyid H.
Sayyid cikin jini, malama cikin jini haka aka kamasu aka tafi da su
da tunanin sun kashe su bisa laakarin su da harbin da suka yi masa.
Dai dai lokacin da suke wannan aika aika suna kuma Yada zantuka
da suka Sanya yan uwa rage motsi ko yunkuri ta hanyar cewa
Sayyid baya gidan, duk da ba a kan wannan nake son magana ba.
Duniya tayi caaaa akan wannan taaddancin amma a Nigeria
musamman a AREWA sai muka JI shiru babu wani motsi Sai yan
uwa da suke kira da FREE ZAKZAKY, said kuma Masu tausayawa
jifa jifa.
Abin takaici wasu kuwa farin ciki suke domin an kashe musu
makiyan su, inda har suka nada jagoran makisan ya zama ya zarce
duk maluman su matsayi wato sayyadi brutai Kamar yadda suke
fada.
Sai dai hakika Allah ya nuna kishin sa kuma ya nuna ikon sa a
wannan hali da muka tsinci kanmu.
Abu na farko shine barin Sayyid ZAKZAKY H da ransa, sannan ita
ma mujahida zeena Allah ya barta da ranta, lalle wadanda suka
aukar da wannan abu ba haka suka so ba, kawai sun rasa yadda
zasu yi ne a wannan lokacin.
Sannan Allah ya sanyawa yan uwa nutsuwa bai bari sun dauki wani
matakin da zai tabbatar da sharrin da suke son lika mana ba.
Ta bangaren yan Nigeria kuwa dai dai wannan lokaci suna dakon
zuwan 2016 ne domin su sharbi Roman dimokradiyya.
Hakika a nan ma muna tsammanin lalle Allah ne ya nuna kishin sa.
Domin 2016 ta shigo da matsatsin rayuwa da talauci.
Jinyace Jinyace Masu shanye jini.
Tsadar kayan masarufi da rashin kudi.
Faduwar tattalin kasa da Faduwar darajar naira.
Tada kayar baya na nja delta /avengers.
Da dai sauran halin kunci da kasa da yayan ta ke ciki har yau 12 12
2016,.
Dole duk mai nazari yayi tunanin cewa me yiwuwa duk wadannan
abubuwa na faruwa sakamakon wannan jini na bayin Allah da aka
zubar a wannan kasa mai ikrarin gwamnatin canji.
Wani abin mamaki shine da aka yi wannan ta'addancin days kuma
halin da ake cikin, su AZZALUMAI ba sun hakura bane,.
..
Sun shekara guda cur suna zubar da jinin mu da musguna mana
Wanda yauma bama fidda ran zasu gwada duk da ba haka muke
fata ba.
MASHA ALLAH, zuwa yanzu jamaar kasa da yawa sun fahimta, sun
gane an zalunce mu ne, musamman bayan hukucin da wata kotu a
Abuja ta yanke na cewa a Saki Sayyid ZAKZAKY H a kuma biya shi
diyya.
Amma harda haka wani yunkuri wannan gwamnatin ke yi na ganin
Sayyid ZAKZAKY H baya nunfashi.
Amma lalle Allah yana kishin Sayyid ZAKZAKY H, in munce haka ba
Wai baza ku iya kashe shi bane domin Shima ya sha fada cewa an
kashe wadanda suka fishi, Amma dai muna son ku San waye ne
kuke yunkurin kashewa?
Mujaddadi ne ne na gwagwarmayar gyara zukatan alumma,.
Sannan mujaddadi ne na tabbatar da addinin musulunci a kasa ta
hanyar gyara Kai.
Babba ne daga cikin mataimaka imam MAHADI AS.
Nasan kun sani mutum ne na musamman.
Me yasa baza ku hakura ku sallama ba??!!
12/12/2016 =12/3/1438.