Allah Yana Son Masoya Manzo (saw)
Ma'asumah Nigeria News Update
Ishaq Sokoto
To kunga kenan shi wannan Manzon ba zaka taɓa kwatanta shi da wani Manzo ba ma, ballantana wani mutum, saboda shine Kamilin samfuri na Mumini. Kuma duk abinda ya aikata da duk abinda ya faɗa, da duk abinda ya tabbatar duk sako ne, shi akan kansa sako ne.
Masu ganin Manzon Allah a matsayin Ɗan saƙo kawai, wai ya isar da saƙo ne, sai muce to da sauran su, don naji ma har akace akwai wani wai yana kamanta wai Annabi da wai ambulan. Wai kamar ambulan ne, wai aka saka wasika, wai in zaka zare wasiƙar itace muhimmiya ba ambulan ɗin ba, wato kaga ambulan ɗin sai ka yar. Saboda haka su a wurin su shi ba Manzon Allah ake bi ba, saƙon ake bi, su ba ruwansu, ba Manzon Allah suke bi ba, to sai muce ayya wannan ɓata ne, Mu Manzon Allah muke bi, shine saƙon. Ina kaga saƙon har da zaka bi saƙon kai kuma? An wurgo maka ne ko kaima Annabin ne?
Tunda Allah Ta'ala haka yaga dama, bil hasali ma abinda Allah Ta'ala yaga bisa wannan Manzon Allah ya wuce nan, yaga dama cewa ta hanyar Manzon ne yaga za'a bauta masa, in kace me yasa haka? Sai Ince haka Allah yaga dama, in kaji haushi ka fashe ka mutu, amma haka Allah yaga dama, baka da yadda za kayi, haka Allah yaga dama, ba za'a bauta masa ba, baza aje gareshi ba sai ta hanyar wannan Manzon, kuma yayi haka nan saboda yafi son Manzon Allah fiye da komai.
Saboda haka tunda yana son Manzon Allah, to yana son Manzon Allah ya tattara masoyansa su zo gareshi, saboda haka hanyarka guda ta samun tsira itace kabi Manzo, kaso Manzo, kayi koyi da Manzo, shikenan kabi Allah, kabi Manzo, haka Allah yaga dama in kace min don menene? Sai in ce maka haka Allah yaga dama. Kuma ba wanda zai ja da abinda Allah yaso.
Ma'asumah Nigeria News Update
Wakilin mu na Sokoto
Tags:
Muhimman zantuka