Jibril Usman sarki
Tun daga lokacin da wannan bawan Allah yafara da'awa sirriya a lokacin yana jami'a a shekarar 1977, a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria (main campus) zuwa lokacinda yafito fili ya bayyana bara'arsa da wilayarsa zuwaga Allah t kadai, a shekarar 1980 a funtua wanda akecema (funtua declaration) tundaga wannan lokacin harzuwa yau dinmu wannan bawan Allah baiyi kasa a guiwaba, yana fadi tashin samarma wannan al'umma yan'ci da nunardasu ubangijinsu. Shekara kusan 40'kenan cur yana wannan da'awa, amma akasarin wannan al'umma baku karba kirannan ba, sai kalilan daga cikinku sune suka karba masa.
Sunnar Allah t bata chanzawa, abin mamaki ga wannan al'umma shine a lokacinda yafi dacewa dasu karbi kiran su amsheshi hannu biyu a lokacinne kuma sukafi nuna kiyayyarsu da wannan al'amarin, ajib al'amarinku, a lokacinda yakamata ace kunnuna tausayinku da kaunarku ga wannan bawan Allah, da kusanto da zuciyarku da jikkunanku gareshi, a lokacinne kukayi nisa kuka taimaki azzalumai da babban azzaluminda tunda aka kafa wannan kasa ba'ataba mugun mutum irinsaba.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Allah t ya lulaku ya tattaraku ya jinginardaku sakamakon ya samar maku da maikira mai gargadi gareku kunki ku karba, shi kuma ya tattara al'amarinku yabarwa kawukanku yabarku da azzalumanku subaku abinda kuke ganin Allah t bazai iya baku shiba.
Allah t yanada hakuri kuma yanada tausayi, yau da zaku nemi gafarar ubangijinku akan fusatashi dakukayi saboda anzalunci Wanda Allah t dakansane yazabeshi domin yatseratarda rayuwarku ta duniya da lahira, kuyima wannan mugayen mutanen bara'a alal akalla akan wannan zaluncinda kuka hadu kuka aikata, da Allah t yasaukarda rahamarsa da tausayinsa ga wannan al'umma.
Bawani abu bane yajawoma wannan kasa da shugabanta halin kaka nikayi, illa fushin Allah garesu, kuma tabbas sai annemi sulhu da Allah kafin a fita wannan matsalar, tahanyar ba waliyinsa yan'cinsa da sauran almajiransa da yima wadanda suka aikata tofin Allahtsine.
Allah t katausaya mana da fitowarsu sayyid zakzaky h, Allah t kafaranta mana da ganin bayan wadannan mugayen mutanen wadanda suka zalunci waliyinka, Allah t ka'amfanardamu.