Allah na Alfahari da Imam Aliy (a.s) Fiye da Mala'iku (a.s)


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @Shafi Domin Kai da Al'ummar ka

IMAM (A.S) YA SADAUKAR DA RANSA DON FANSAR RAN ANNABI (S.A W W).
Mala'iku bayi ne na Allah wadanda ya dora musu aiki da ba su da zabin yinsa ko barin sa, wannan dalili yasa su babu hisabi a kansu.

Su kuwa 'yan Adam an ba su zabi na yi ko rashin yi, tare da nuna musu sakomakon abinda suka dauka daga cikin biyun.

" LALLE MUN SHIRYAR DA SHI TAFARKI, IN YA SO YA GODE KO KUMA YA KAFIRCE."
Yayin da kafiran Makkah su kayi qoqarin daqile da'awar Annabi (S A.W.W) kuma su ka ga al'amarinsa sai qara tumbatsa yake, sai su kayi yunqurin kashe shi don kawo qarshen kiran nasa.

" YAYIN DA KAFIRAI SU KE YIN MAKIRCI GARE KA, DON SU TABBATAR DA KAI KO SU KORE KA KO KUMA SU KASHE KA......."
To, a wannan lokaci ne Allah ya umarci Annabi (S) cewa yayi Hijra shi da jama'ar sa zuwa Madinah. Sai ya kira Imam Ali (A.S) ya umarce shi cewa ya kwanta akan gadonsa don ba shi kariya a daidai lokacin da ake neman ransa (S).

Malaman hadisai sun kawo cewa cikin daren nan Allah yayi wahayi zuwa ga Jibrilu da Mika'ilu (A.S) cewa;
" NI ZAN HADA 'YAN'UWANTAKA A TSAKANINKU, KUMA ZAN SANYA RAYUWAR 'DAYANKU TA KASANCR MAFI TSAHO KAN TA 'DAN'UWANSA, TO, WANENE ZAI FIFITA RAYUWAR 'DAYANSA TA KASANCE ME TSAHO KAN TASA?"

Dukkansu sai kowa ya zabi rayuwarsa ta kasance mafi tsaho kan ta dan'uwansa.
Sai Allah (T) yace musu;
" ASHE YANZU BA ZA KU KASANCE KAMAR ALIYU 'DAN ABIY 'DALIB BA? NA HADA 'YAN'UWANTAKA TSAKANINSA DA MUHAMMADU, SAI YA KWANTA KAN GADONSA YANA FANSAR SA DA RANSA, KUMA YANA FIFITA SHI DA RAYUWA. TO, KU SAUKA KAN QASA KU BA SHI KARIYA DAGA MAQITANSA."

To, sai Jibrilu ya tsaya a kansa, Mika'ilu kuma ta sawunsa (qafafu) suna cewa;
" BAKKHIN-BAKKHIN MIN MITHLIKA YAA IBN ABIY 'DALIB, YUBAHIL-LAHU BIKAL MALA'IKATU."

" Da kyau ! Da kyau !! Yaa dan Abu 'Dalib, babu wani kamarka, Allah na alfahari da kai fiye da Mala'iku."
-Nurul-Absar, Sh:140.
-Tafsirul-Kabir na Fakruddeen Razi, J:2

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post