Aiki domin samun tabbaci na shiga Aljanna!!



Domin samun tagomashi da wannan babban rabo na shiga aljanna, saika yi aiki aikin nan kuma bazai zam aiki mai sauki ba

Domin duk yadda kaji ance akwai tago mashi mai tsoka, zaka tarar saika fiskanci wahala, sadaukar da lokaci, da cire son zuciya.

Amma wannan hanyoyi ne da idan mutum ya kiyaye su ya damfaru da aikata su zai sami garantin lasisin shiga Aljanna daga bakin masoyinmu Manzon Allah(S).

Karanta wadannan hadisai kaji daga bakin da baya karya.....


Manzon Allah (S) yace; "Duk bawan da ya kiyaye abinda ke tsakanin gemunsa (halshe) ya kuma kiyaye abinda ke tsakanin Cinyoyinsa, zan kiyaye mishi mazaunin sa a gidan Aljanna".

A wata ruwaya kuma Manzon Allah (S) ya fada cewa; "Da wani bawa zai gaba tomin da wasu abubuwa guda shida, ni kum azan gabato masa da gidan aljanna.

Ga abubuwan  kamar haka:

Idan zaka yi magana kada kayi qarya.

Idan yai alqawari, kada ya saba.

Idan aka bashi amana, kada yayi ha'inci.

Sannan ya kiyaye sha'awarsa,  al'auransa ya kuma hana hannayen sa da halshensa aikata sabawa mahalicci."


Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhamamad.


Allah ya kara kare mu ya kare mana zuciyoyinmu da ingiza mu zuwa aikata sabawa mahalicci.

Dalibinku
Bin Haroun Sigau
08065008703

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post