✍️ADAM LAWAL KATSINA
Wannan yana daga cikin abubuwan da ya Addabi Musulman Duniya
"Shehu Dahiru Usman Bauchi ya bada Sako zuwa ga Gwamnan Bauchi, Kai Gwamna ga Sako na ka gaya ma Buhari ya saki Malam Zakzaky (h). Ka gaya masa ni nace ya saki Malam Zakzaky. Masifun kasar nan sakomakon rike wannan bawan Allahn ne, saboda haka kace inji ni ya saki malam zakzaky ya gaggauta sakin Malam Zakzaky".
To Allah ya sakama Shehi, ya tsawaita Rayuwar Shehi, kuma ya yawaita irinsa a Almajiransa da dukkan mabiya, domin abun da muke bukata kenan, kuma shine muka rasa. Abin da muka sani ka'ida shine Malamai sune Jagororin Al'umma, Shuwagabanni da Sarakuna ne ke shugabantar da Al'umma su kuma Malamai ne ke Jagorantarsu.
Gudanar da Al'amurra yana hannun Malamai ne wadanda suka san Halal din Allah da Haram din Allah. Abin da Allah swt yake cewa "Wa Kalmatullahi iyal Ulya wa kalmatul kukhfuri iyaa sufulah" Kalmar Allah swt ita ce sama, kuma wadanda aka sani da kalmar Allah awajensu sune Malamai. Malamai ne suka san kalmar Allah suka san muradin Allah, su sukan abin da Allah ke so ayi, duk wata Kalma da ba ta Allah ba ko wacece a kasa take Sufulah ce.
Amma yanzu abin takaici wadanan Jahilan sune ke juya Malamai, Karuwa ce ke cema matar Aure ga yadda ake zaman Aure, ga yadda ake Mu'amala da Miji. ku fadamin ta ina karuwa zata gyara matar Aure? to taya Jahilai zasu gyara Malamai har su gudanar dashi.
_Shaikh Yaqoub Yahya a wajen Taron Makon Hadin Kai wanda akayi a garin Katsina Alhamis 28Nov2019.

Tags:
Daga marubata