Abubuwa hudu da dabbobi ke iya shaida su!!!

 A rayuwar dabba zaka sha mamakin yadda suke da sabo da mutum hakan yana biyo bayan kyautata wane da ake musu.

Kuma ainihin abinda suka ginu akai suke iya shaidawa sune abubuwa guda hudu.

Yazo a ruwaya cikin littafin Al-Kisal, na sheikh Saduq, Shafi na 422. Imam Sajjad (As) yace; "Abubuwa  hudu da dabbobi kan iya shida wa sune:

Allah madaukakin sarki daya halicce su, Mutuwa, Mata da Mazan su, sai abu na hudu shine; Makiyaya (Masu kula dasu).

Hakika, Allah mai hikima ne daya tsara musu yadda zasu saba da masu kula dasu, hausawa sunce; zuciya tana son mai kyautata mata ne.

Wannan ne yasa ka Allah daya halicce su ya kimtsa musu sanin sa da sanin mai kyautata musu, hadi da komawar su zuwa gareshi da sanin jinsin. Su san juna don tafiyar da rayuwa cikin tsari.

Allah mai iko.......

Sharhi

Lallai, ko wannan muka duba zamu ga cewa, fifikon mu da ababen halitta wata babban daraja ce da Allah yayi mana.

Tambaya!!

Me yasa zamu kasa kode masa ta hanyar yi masa da'a da iklasi?
Ko mun manta cewa gareshi zamu koma ne?
Ya zata kasance inka zam cikin masu sabawa mahaliccinka gobe kiyama?

Lallai, zama bai ganmu ba, barci ba namu bane dole ne mu tashi tsaye mu bauta wa Allah kamar muna ganinsa. Matuqar zamu kasa aikata haka nan ba mu zama masu godiya ga ni'imar Allah ba, kuma lallai, babu makawa Allah ya tana di azaba mai radadi ga wanda suka bijire masa.

Allah ya tsare mu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post