Abin da Zakzaky keyi, Jaddada kiran Manzon Allah (S) ne!!


Kamar yadda Makiya Manzon Allah, makiya addinin Allah sukai ta hankoron ganin bayan Manzon Allah (S), hakane ke faruwa da Sheikh Zakzaky (H).

Menene laifinsa? Sabida yana kira a koma ga hanyar Allah ta gaskiya. Babu wani abu a tarihi daya faru damu wanda kafin hakan bamu ganshi a taririn manyan bayin Allah ba. Wannan shike kara mana kaimi wajen ganin sai munyi nasara kan kiran al'umma da tabbatar da gaskiya tsakani.

Shi Azzalumi kullum gani yake zai nasara akan wanda yake hankorin kaiwa gareshi, mu kuma a tafiyar mu babu wani abu waishi fadi (Rashin nasara) kullum mumini nasara yake ci a tafiyarsa.

Nasarar nan a nan duniya ne ko ko a gobe kiya ma ne zai girbi nasarar, koma dai yaya ne nasara tamu ce, in kun kashe mu, munyi shahada zamu tashi a cikin wadanda aka zalunta tare da samun rabo mai girma.

In kuma mun mutu mun koma ga Allah muna masu yakini da aiki bisa iklasi. To, kodai kun kashe mu ku sani akwai yaya yenmu wanda in kuka ce zaku kashe dukkan wani dan Shi'a ne tabbas kunsan abu ne da bazai yiwu ba.

Zaku dai iya kashe wanda Allah ya ga damar ya yarje muku ku kashe amma ku sani baza ku taba iya dusashe hasken addinin Allah ba, wannan addinin da muke kira akai kayan Allah ne kuma shi zai tsare kayan sa bawai iyawarmu bane ko dibarar mu.

Mu namu kawai bin umurni ne, da aiki domin samun tsira da sauke nauyi a wajen Allah. Ban taba ganin wanda a tarihin wannan kasa yake fiskantar azaba da gallazawa kamar Sayyid Zakzaky (H) ba, wannan ya kara tabbatar mana yana kan gaskiya.

Abubuwan kuma da kuke mana suke kara kambama kiransa a fadin duniya, domin ta hakane kuke kai wannan kira wajen da mu bazamu iya kaita ba.

Alhamdulillah shekaru sama da talatin zuwa arba'in Sayyid yana kira kan hanyar Allah kuma bai taba cenja wa.

Mun gode maka ya Allah daka nuna mana wannan mai kira, fatan ka tabbatar damu tare dashi muna masu imani da kara kusanci zuwa gareka badon halinmu ba, alfarmar Manzon Allah (S).

A karshe ina kara Kira ga wannan azzalumai dasu sake Sayyid Zakzaky ba tare da kaidi ko sharadi ba.

#FreeZakzaky
#FreeUmmaZeenat
#WeDemandJustice

Bin Haroun Sigau

08065008703

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post