Kafin infara cewa komai zanso inyi shimfida da wasu zantuka na jagoranmu Malam Zakzaky (H) da yayi su tun shekaru goma sha hudu da suka shude.
Malam yace; "Suna bukatar kawai watarana ne yadda zasu dira su fara kisan kare dangi, (bama fatan haka nan ya auku),amma ya kamata mu farka kafin fargar jaji, domin idan farkawar ya zama mana ta dole to yanada wuyar tayi amfani. Irin abinda ya faru a Afghanistan kenan, anfarkar da su ne ta karfi da yaji, anshiga kasar ne kawai basu ankara ba sai gashi kawai ana salladuwa a kansu, sannan suka farka a yayinda aka gutsire kai."
Maulana Sayyed (H) yakuma ce, "Tun yanzun, tun basuyi mana bane zamu farka, a san inda muka sa gaba. Ballantana mu anan inda muke da tarihin addini, muka gaji addini, addini muka sani, shikuma bature da yazo ya kama kasar nan da karfin tsiya ya dankara mana ingilishi, yazo ya samemu da addini ne. Kuma yasan lalle shi addinin nan ne yake tare damu, kuma har yanzu yana nan a jininmu da zukatanmu.
To tun ba a wuce wannan mikdarin AAnje wata marhala da zamu samu kanmu a mawuyacin hali ba, mukoma ga addini, kuma a daina tunanin akwai wata hanya sassauka ta komawa ga addini. Sunna ce Kwara daya rak,Sunnar Allah wacce bata canzawa, yanzu ba addini ke iko ba al'ummar musulmi suce basu yarda ba. Addini ne kawai zaiyi iko akansu. Muga wanda zai iya dankara musu wani abu."
Malam Zakzaky (H) yakuma ce, "Shine muke kira ga Al'umma a dake ne a tafarkin Allah a daina kwamacala. A daina shiga sabgar wadannan mutane da suka bace suke batar da Al'umma."
Mafi akasarinmu 'Yan uwa muntafi akan wannan waki'ar da ta samemu internationally ce, waki'a ce babba,wacce muke ganin kasa da kasa ne musammam manya suka hadu da karamar kasa ta Najeriya suka afkamana da kisan kiyashi. Sunkashe jarirai sun kone su,sun kashe tsofaffi,matasa, yara, mata da maza sun kashe, wasu ansa musu fitar da ransu anbanka musu wuta kiri-kiri sunaji Suna kallo suka cinye kurmus, su kazama toka, sunje sunyi ruwan wuta akan maaminmu bayan sun kashe masa yara uku rigis akan idonsa tareda harbin matarsa. An daukai cikin jini, ga raunuka a jikinsa sunje sun ajeshi babu kulawa ga wani rauni a idonsa yana masa zafi da zugi, hannunsa an ratata dashi gamida wasu alburusai a jikinsa wadanda kullum kara ma Malam Ciwo suke.Shekaru hudu (gyara) kenan Malam yana dauke da wadannan raunukan mukuma da yawan mu yakai milyan ashirin muna gidajen mu a kwance ba abin da ya shafemu, sai walwala muke da dagawa cikin suturu masu kyau. Yayinda jagora na can rai a hannun Allah.
Munkasa yin komai, eh mana munkasa komai mana bayan yau idan kaje markaz wurin da ake addu'ar Allah ya karawa Malam lfy,ya kwato sa mutane kalilan zaka gani, uwa-uba ma abinda mukeyi na muzaharori cikin kashi dari na 'yan uwan dake garin da suka fito muzahara bazaka samu kashi 30 ciki ba. Yanzu wannan abinda mukeyi ya dace kenan? Kuna ganin shirun mu dinnan shine zai sa su saki Malam (H)?, Wallahi shirun mu su keso suji, sukuma su aiwatar da kudurinsu akan Malam na kisa! Kai dan uwa kayi tunani wacce uwa zakayi a duniya babu jagora, ko dai mun manta ne Malam Shine gatanmu? Ashe idan muka bari aka cutar dashi Allah bazai Tambaye mu ba? Kowannen mu ya shirya amsar da zai ba Allah na cutar da Malam da muka bari akayi. Salihin mumini Malam turi yaki bari a aikata kuskure dashi, rayuwarsa ya mika akan Malam. Kunga hakkin sa ya sauke mu da muke yanzu 'Yan uwa ashe bazamu mika tamu ba mu sauke hakkin dake kanmu! Ko shikenan tunda anka ma Malam sai muyita cewa Allah ya kwato mana shi, kuna ganin ba aikinmu bane zai sa Allah ya taimake ya kwato mana malam?
To wanne irin aiki mukeyi a yanzu, muzahara ko addu'a? Da yawan 'Yan uwa idan aka bada addu'oi basayi sai dai kaji sunce wai sunyi yawa, Wasu kuma cewa sukeyi Allah ya tausaya mana ya kwato mana Malam. Haba dan'uwa wanne irin tausayi ne Allah baiji namu ba ko so kake sai kaga mala'iku sunje Abuja sun taho da Malam! Wasu kuma da zarar ance za'ayi muzahara musammam a cikin garin Abuja sai kaji sunce Akwai yanayi, wasu kuma InshaAllah suke cewa,kememe dan uwa/ 'Yar uwa sai suki zuwa muzahara su fake da wai babu kudi. Lalle wannan ba uzuri bane kamar yadda Malam Kasim Umar Sokkoto ya fada yace; "Rashin kudi ba uzuri bane, Uzurinka guda daya ne kawai ace kana kan gadon asibiti bakada lafiya, amma ko a kafa kaje inda ake fafutukar ganin ansako jagora kuma kowa aje dashi harda kananan yara, kai harda na ciki wanda baizo duniya ba indai uwar ba nakuda take yi ba."
Lalle Akwai kalubale a garemu 'yan uwa me girman gaske, wanda ya zamar mana wajibi mu ja 'damara mu tunkare su.
Malam Zakzaky tabbas yana cikin hadari tunda har yanzu bai samu ganin kwararren Likita ba. Ko bamuji Malam yace da aka kaimai ziyara Har yanzun idon da aka har bar mai yana masa zafi ba.Dan uwa/ 'Yar uwa ya kike ji idan haki ya shiga cikin idon ka/ki to ina ga wanda Alburushi ne ya shige ya fitar da idon, yadauka da kansa ya maida sa.Gaskiya mu mabiya zama ba namu bane, addu'oi muzaharori su suka kamacemu. Yakamata da mukaji wannan labarin ya caza mu mufito duk cikarmu mu shiga Abuja mu firgita azzalumai mu nuna musu lalle mu 'yan halas din Malam Zakzaky (H) ne kana muja kunnuwansu, mu firgita su ta yadda cikinsu zai duri ruwa ta hanyar kururuwanmu a cikinsu muyi musu gargadin su kuka da kansu duk Abinda yafaru da Malam su ma sai ya faru dasu.
Allah yakarawa Malam Zakzaky (H) Lafiya.
Wannan Ra'ayina ne ba ra'ayin Harka ba.
Munyi copy ne daga Rubutun Muttaqah kumasy Shekaru biyu da waki'ar nan
muttaqahkumasy@yahoo.com.