Zabar Macce Tagari ga Namiji



Tare da Bashir_Adam

Ko wani dan Adam yana da burin ya auri mace ta gari, koda kuwa shi ba miji na gari bane, domin kowa ya yarda cewa mace ta gari alheri ce ga mijinta.


Matakin farko na samun mace ta gari shine kai Ka fara zamowa mutum na gari. 

Yayinda Ka zamo mutum nagari, to anan ne ake saran kasamu mace ta gari, domin da icce mai kama akeyin Qota.


Jikan manzon Allah (s) Imam sadiq (as) yana cewa: abubuwa Uku hutu ne ga mumini, yalwataccen gida, da mace ta gari, mai taimakonsa akan al'amurran duniya dana lahira.

Daga cikin alamomin mace ta gari (kafin aure), akwai zamowarta mai Tarbiyyah, kunya, nutsuwa, ilimi, da lizimtar addini.


Bayan aure kuwa, akan gane mace ta gari ne ta hanyar kyautatawa mijinta, da rashin dora masa wahalhalu da dawainiyoyi, da rashin yi masa gori, da rashin kushe duk wani koqarinsa.

Sauran sun hada da taimakonsa, manzon Allah (s) yana cewa jihadin mace, shine kyautata zaman aurenta.

Farin ciki ya tabbata ga mijin mace ta gari.

INA BARAR ADDU'A AKAN DAMUWA NA ALLAH YA YAYEMIN GA DUK WANDA YA KARANTA WANNAN RUBUTUN NAWA

1/2/2018

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post