Yazo cikin littafin Kanzul Ummal, lamba ta 43134. Manzon Allah (S) yace; "Idan kofar aikin kwarai ta bude wa wani mutum, yayi kokarin amfani da ita, domin baisan yaushe zata kulle ba."
A wata ruwaya kuma, Manzon Allah (S) ya kara cewa; "Barin dama ta kufce maka, yakan haifar da dana sani".
Imam Ali (As) ya fada a wata ruwaya, "Dama wuce wa take da sauri kamar wucewar girgije."
Imam (As) ya kara da cewa; "Dama saurin wuce wa gareta, sai wahalar dawowa."
Imam bai gushe ba yana cewa"Rasa dama abin bacin raine".
Imam Sadik (As) yace; "Duk wanda ya sami dama ya tsaya dogon binciken wasu lamurra, rana ku masu wucewa zasu tafi da damar sa. Sabida ba sabon abu bane ranaku su tafi da damar da kake da ita, kamar yadda lokaci ke tafiya da damammakin mutane."
╰➝➝Sharhi
Ya 'yan uwa na maza da mata zamanin samartaka dama ce babba na neman kusanci zuwa ga Allah (T), lokacin ne kake da karfin da zakai ibada ka kusanci Allah da kyawawan ayyuka.
Hausawa na cewa; "Idan kaga tsohon banza, to dama yaron banza ne. Domin daga yaron banza ake samar da tsohon banza."
Duk tsohon da zaka yaje wajen rawan banjo da me asharalle ka ganshi to, zaka samu lokacin samartakan sa mai yawan ziyartar casu da rawe-rawe ne.
Kar ka bari shaidan ya yaudari zuciyarka, kamar yadda yake yaudarar wawaye. Domin ba wanda zai zam mai yiwa son ransa biyayya zuwa ga aikin shaidana sai wawa.
Rayuwar nan baki dayanta gwaji ne, munzo ne a gwada mu gobe kiyama mu karbi sakamakon abinda muka kasance muna aikatawa a wannan duniyar.
Allah ya datar damu, ya karemu ya kare mana Imanin mu.
Naku har Kullum
Bin 卄α尺ουπ 丂ιᎶαυ.
08065008703
Tags:
Tunatarwa