@MA'ASUMA NIGERIA NEWS UPDATES
MNUSCD : 037
A Jiya Asabar 22/11/2019 , dubban al'umma musulmi maza da mata. Na garin Bangi dake a karamar hukumar Mariga, a cikin Jihar Niger. Suka gabatar da zagayen Mauludin fiyayyen halitta (S.A.W).
An dai fara wannan muhimmiyar ibadar ne Jiya Asabar da misalin karfe 10:00am na safe. Inda taron ya hada dukkanin bangarorin musulmin garin Bangi da sauran kauyukan ta. Inda har Yan uwa Almajiran Musulmi Sheikh Ibrahim Yaqub Zakzaky (H).
Sai dai Mauludin ya kasance a cikin tsari da nizami. Inda duk Wanda ka gani a wurin yaci kwaliyya da a domin domin wannan ranar. Kuma masu wannan Muzaharar suna tafe suna rera wakokin yabo ga fiyayyen halitta Manzon Rahma (S.A.W).
A gefe daya kuma ga masu kallo suna ta nuna jin dadin su. Musamman lokacin da Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky suke tafiya. Duk inda Suka wuce zaka ana cewa "Allah ya saka muku ,Allah ya fito muku da Malamin ku." To haka dai MUZAHARAR ta cigaba da gudana har zuwa karfe 3pm da wasu yan mintoci.
Wanda daga bisani aka kammala muzaharar a babban Masallacin juma'a na garin Bangin. Inda malamai daban daban ne Suka gabatar da jawabi a wurin. Inda daga karshe aka gabatar da wakilin Yan uwa Almajiran Sheikh Zakzaky na garin Bangin, Malam Abdullahi Bangi ya yi ta'aliki. Sannan aka yi addu'a aka sallami mahalarta.
Wannan kadan kenan daga cikin Abinda ya ya guda Jiya a garin Bangi.
Tare da wakilinmu
Auwal M Tukur
24/11/2019
Tags:
Munasabobi