Yabo ga Masoyi Yana Daga cikin Kyawawan dabi'u..!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

A ko da yaushe muslinci na koyar damu ne abinda zai amfane mu a duniyar mu da lahirar mu, matuqar mutum ya bi wannan koyarwa zai ga alkhairi a dukkan rayuwar sa.

Daga cikin kyawawan dabi'u akai:-

YABAWA MASOYI:- Duk mutumin da ya nuna maka so bai kamata ka kasa nuna masa godiyar ka ta hanyar yabonsa ba, domin yabon da za ka riqa yi masa zai sa ya qara sonka cikin zuciyar sa. Idan kana musu ka yabi matarka ko budurwar ka ko kuma abokinka na gaskiya kaga yadda sonka zai qaru cikin zuciyar ta/sa.

TAIMAKON WANDA YA BUQACI TAIMAKO DAGA GARE KA:- Duk wani taimako da za ka yiwa mutum kan faranta masa rai, amma mafi girma shine wanda ka yiwa wanda ya buqaci taimakon naka a daidai lokacin da ya buqata. Yin haka zai faranta masa rai fiye da ka ba shi taimako ba tare da ya nema ba.

GAFARA GA WANDA YA CUTAR DA KAI:- Umarnin Allah (T) da ya umarce mu kan cewa mu riqa yin yafiya ga wanda yayi mana ba daidai ba, inda yake cewa;

" KUYI YAFIYA KUMA KU KAU DA KAI, SHIN KO BA KU SO ALLAH YA GAFARTA MUKU NE?"

Wannan aya na karantar damu ne cewa in dai mutum yana son gafarar Ubangijinsa, to, ya kasance mai yin gafara ga wanda ya cutar da shi, domin shi ma mai sabon Ubangijinsa ne a kullum.

NISANTAR WANDA YAYI WATSI DA KAI:- Daga cikin kalaman hikima na Imam Ali (A.S) yana cewa;

" IDAN KA GUJI MAI JANKA A JIKA TO, KA YI ASARAR WANI RABO GWAGGWABA, IDAN KUMA KA NANIQEWA MAI WATSAR DA KAI, TO, KA KUNYATA KANKA."

Wannan kalma ta hikima na karantar damu ne cewa kada muyi watsi da wanda ke janmu a jika, domin soyayyar sa gare mu yasa shi yin haka, kaga kuwa masoyinka ba zai taba son ganin abinda zai cutar da kai ba. Shi kuma wanda wanda ke yin watsi da kai ba ya qaunar ka ne, saboda haka matuqar ka naniqe masa wata rana zai kunyata ka cikin jama'a, domin bai damu da yin mu'amala da kai ba, wataqila ma maqiyi ne gare ka.

ALLAH YA AMFANAR DAMU 'YAR WANNAN TUNATARWA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda

       08126385470

~ 19th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post