HAKAN TA FARU NE SAKAMAKON ZAGIN SAHABBAN DA YAKE YI....
Wannan ita ce maganar da ke yawo cikin bakunan 'yan Izalar garin Ningi don qara bayyanar da sharri da kuma hatsayin da ke cikin aqidar 'yan Shi'ah.
Shin, hakan ta faru da gaske ne ko kuma dai irin qaryar da suke yi ne na cewa 'yan Shi'ah na da Qur'ani kuma suna zagin Sahabbai?
GASKIYAR ABINDA YA FARU
―――――――――――――――
Wata rana qanin babana ya bani tsohuwar wayarsa (Phone)irin ta da (old modern)don nema mata battery, to, da naje wajen masu saida wayoyi sai suka ce sai dai a zo da tsohon battery bata zai fi sauqi wajen samun irinsa.
To, da shike kan battery din ya daye har wata waya (wire)na bayyane a fili, kuma na sa shi cikin aljuhu nane tare da wani biro, na sanya hannuna cikin aljuhun don na ciro biro din sai kan biron ya hadu da wayar battery, kawai sai suka yi (spark)wanda yasa nayi saurin fitowa da hannuna kuma har wutar battery din ta huda min aljihun rigar tawa.
Wannan abu ya faru ne a gaban wani dan Izala yayin ziyara dana kai masa wacce muke yiwa juna, kuma ko ban kira shi abokina ba zan ce wanda muke mutunci da shi.
Da nake bawa qanin baban nawa labarin abinda ya faru sai yace min ai shima a hannunsa batterin ya kama da wuta.
Da faruwar wannan abu ya kai shekara uku, amma har yanzu maganar na yawo cikin 'yan Izala suna cewa;
‘’ AI AKWAI WANI 'DAN SHI'AH MAI YAWAN ZAGIN SAHABBAI A (F.B), GANIN KIRKIN DA YAKE DA SHI SHINE WASU MATASAN IZALA SUKA KIRA SHI DON YI MASA NASIHA, AMMA KAWAI SAI WUTA TA TASHI CIKIN ALJUHUNSA ‘’.
Don kaucewa zargi, kai tsaye ba zan iya cewa ga wanda ya fara yada wannan sharri ba.
TAMBAYA
――――――
- Me yasa irin wannan sakayya ba ta taba faruwa cikin masu cewa Allah uku bane?
- Ashe zagin Sahabbai ma na cikin munanan ayyukan da Allah ke gaggauta daukar musu fansa tun daga nan duniya?
Idan amsa ita eh ! Sai nace;
YAA ALLAH KA TSINEWA YAZEEDU BN MU'AWIYAH, KA KUMA TSINEWA MU'AWIYA GWARGWADON ADADIN TSINUWAR DA SUKA YIWA IMAM ALI (A.S)A KAN MIMBARI.
Tags:
Tunatarwa