Wata Sabuwa:- Kisa ne Hukuncin Wanda ya qi bayar da Zakkah a musulunci !!;


Kuma Wai cikin Sahihul Buhari...

DAGA HUKUNCE-HUKUNCEN IBN QUHAFATA

Ba don na ci karo da wannan fatawar ba, haqiqa da na halaka wajen hukunci kan wannan mas'ala.

Abinda na dogara da shi shine, fitar da zakkah na daga cikin abubuwan da Allah (T) ya wajabta ga dukkan musulmi mai ikon fitarwa, wato wanda ya sami abinda nisabinsa ya kai a fitar masa da Zakkah.

Sai dai a qarancin ilimi irin nawa babu wani aikin ibada wanda za a iya kashe mutum a kansa don ya qi aikata shi koma bayan sallah, duk da cewa rashin aikata su zai yi sanadin shigar mutum wuta. Misali,

Barin zakkah,

Barin Hajji,

Barin azumi.

Amma kwatsam sai na ci karo da wannan hadisi na Bukhari mai cewa;

Qutaibata Bn Sa'id ya bamu labari, Laithi ya bamu labari daga Uqaili, daga Zuhriy. Ubaidullah Ibn Abdullahi Bn Utbata ya bani labari daga Abu Huraira yace; Yayin da Manzon Allah (S.A.W.W) yayi wafati kuma aka Halifantar da Abubakar a bayansa, kuma wadanda suka kafirta daga Quraishawa suka kafirta, sai Umar ya cewa Abubakar;

" TA YAYA ZA KA YAQI MUTANE ALHALI MANZON ALLAH (S.A.W W) YACE;  
" AN UMARCE NI DA NA YAQI MUTANE HAR SAI SUN FURTA (kalmar) LAA'ILAHA ILLAL-LAH. DUK WANDA YACE LAA'ILAHA ILLAL-LAH, TO  DUKIYARSA DA RANSA SUN TSIRA DAGA GARE NI, SAI DAI BISA HAQQINSA, SAKAMAKON SU NA WAJEN ALLAH."

Sai Abubakar yace;

" WALLAHI SAI NA YAQI WANDA YA RABA TSAKANIN SALLAH DA ZAKKAH, DOMIN ZAKKAH HAQQIN DUKIYA CE. WALLAHI DA ZA SU HANA NI QARAMIN ABU WANDA SUKE BAYAR DA SHI GA MANZON ALLAH (S.A.W.W) SAI NA YAQE SU BISA HANA SHI  !"

Sai Umar yace; wannan ba wani abu bane nake gani face Allah ne kawai ya yalwata qirjinsa da yaqi (a bayan Annabi), na san cewa yana da gaskiya."

(Bukhari, hadisi na 7284).

Ko da shike wasu sun ce wadan can mutane ba sunqi bayar da Zakkar bisa inkari bane, sai dai cewa suka yi;

" BA ZA MU BAYAR DA ZAKKAH GA WANDA ALLAH DA MANZONSA BA SU CE MU BI SHI BA."

Tare da Ado Isah Guda.

 08126375470-08137925034

~ 23rd November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post