Wasu Daga Cikin Dalilan Talauci
Ma'asumah Nigeria News Update
Tare da Ishaq
Wani mutum ya zo wajen Amirul Muminin Imam Ali (As) yayi masa kukan tsananin talauci da rashin da yake fama da shi.
Sai Amirul Muminin (As) Yace masa: Mai yiyuwa kana magana a bayan gida ko?
Sai mutumin yace: A’a, Ya Amirul Muminin…
Sai Imam Ali (As) Yace masa: Mai yiyuwa kana yanke faratunka da hakwaranka ko?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace masa: Mai yiyuwa kana kiran iyayenka da sunayensu ko?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace masa: Mai yiyuwa kana barin shara da dare a gidanka?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yce: Mai yiyuwa kana barci ba tare da alwala ba?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace: Mai yiyuwa kana shigewa gaban iyayenka a lokacin da tafiya?
Sai mutumin yace: A’a, ba na aikata haka…
Sai Imam Ali (As) ya ce: Wataqila kana share gidanka da dare ko?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace: Wataqila kana yanke faratunka ranar Lahadi ko?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace: Wataqila kana yawaita la’antar Ƴaƴanja? Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka, Ya Amirul Muminin…
Sai Imam Ali (As) Yace masa: Mai yiyuwa kana tofar da yawu (kaki) a cikin bayan gida ko?
Sai mutumin yace: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yce masa: Wataƙila ba lka Bismillah a yayin fara cin abinci da kuma hamdala a ƙarshensa?
Sai mutumin ya ce: A’a, bana aikata haka…
Sai Imam Ali (As) Yace: Mai yiyuwa baka yiwa iyayenka addu’a yayin sallarka?
Sai mutumin ya ce: Na’am, Ya Amirul Muminin. Lalle haka ne.
Ma'asumah Nigeria News Update
Wakilin mu na Sokoto
08132933333
Tags:
Taskar ilimi