Tsohon Shugaban Kasar Nigeria na Fuskantar Barazanar kora Daga PDP.

Zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar a makon da ya gabata na neman ya jefa tsohon shugaban Nijeriya, Goodluck Ebele Jonathan cikin matsala bayan da dan takarar jam’iyyar APC, David Lyon ya samu nasara da gagarumar rinjaye akan takwaransa na PDP, Duoye Diri.
Murna da ‘yan kabilar Jonathan suka yi ta yi bayan da aka bayyana sakamakon zabe ya jefa shakku kan layin da shi Jonathan din ya dauka a zaben, duk da dai akwai wasu hujjojin da suka fi wannan kar da ke nuna cewa Jonathan baya tare da PDP a wannan zabe.
A ranar 4 ga watan Satumba, 2019 aka gudanar da zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP. Sanannan al’amari ne cewa Jonathan baya goyon bayan Duoye Diri, amma gwamna Dickson ya yi amfani da karfin iko ya kakaba nasa.
Madogara:- Legit hausa
.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post