
A shekara goma an cinye naira tiriliyan daya, wato naira biliyan dubu,tsakanin yan'majalissar tarayya, sanatoci da bangaren zartarwa, da sunan aikin mazabu(constituency project).
Majiyata BBC Hausa shirin safiyar ranar.
20-11-2019
Ya ilahi da za'a rabawa mutane kudin nan suje suyi Sana'a mutum miliyan daya za'a ba naira miliyan daya-daya. Amma wasu yan tsirarun mutane sun cinye kudin, sai illa Dan Abu kalilan da ba'a rasa ba Wanda yaje hannun talakkawa.
Kai Dan'uwa bari in kara bude maka abin yadda zaka fahimci girman barnar, a kalla a kowace karamar hukuma za'a ba mutum dubu daya da Dari uku, naira miliyan daya-daya a cikin kananan hukumomin NAJERIYA Dari bakwai da saba'in da hudu, da muke dasu. Amma kasa da mutum dubu daya sun cinye kudin.
Talakka kayi ta kanka shugabannin ka basu da niyyar taimakawa rayuwar ka.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Musa Ibrahim Daura
20-11-2019.
Tags:
Daga marubata
Allah kyauta
ReplyDelete