Wannan itace sunna Zantukan Manzon Allah, Ayyukan Manzon Allah, da Tabbatarwar Manzon Allah, kaga dashi da saƙon duk abu ɗaya, ba maraba, don haka wanda duk ya taba Manzon Allah, ko da dan ƙiris ya taba shi, to ya rusa saƙo ɗari bisa ɗari, ina nufin in ya taɓa mutuncin Manzon Allah ko da Ɗan kaɗan mutum ya nakasta Manzon Allah, to ya rushe saƙon gaba ɗaya, in ma mutum ya lura da kyau, in aka ce maka wanene kafiri? Kace amsa wanda ya kafircewa Manzon Allah, koda yayi Imani da Allah, ai ga waɗansu mutane suna zuwa ranar Lahadi suyi ta waƙe waƙe, ba sun yarda akwai Allah ba? To Musulmi ne? Me ya maishe su kafirai? Basu yarda da Manzon Allah ba.
Shiyasa ma sunansa ya shiga cikin kalmar Shahada. Alhali sunan Manzannin da suka gabace shi ba wanda aka sa shi cikin Kalmar Shahada. Lokacin Annabi Isah (As) ba Cewa ake La'ilaha Illallah Isa Rasulullah ba, sedai ace La'ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu, haka ma lokacin Musa ba'a cewa La'ilaha Illallah Musa Rasulullah, se dai ace La'ilaha Illallahu Wahdahu La Sharika Lahu. Na'am zakayi Imani da Manzon amma sashi cikin Kalmar Shahada be zama lazim ba, saboda dama a lokaci guda ana samun Manzanni da yawa suyi zamani ɗaya, Ana samun Annabawa da yawan gaske.
To Amma shi Manzon Rahama mai tsira da aminci dole ne kayi furuci da sunansa a matsayin Shine Manzo, kace La'ilaha Illallah Muhammadur Rasulullah lazim ne in ba haka ba, baka ma da Imani, wato ba ina nufin inka faɗa kawai ba, wato mutum yace yayi Imani da Allah kawai amma bai yi Imani da Manzonsa ba, to bai yi Imani ko da ɗaya bisa ɗari, ba shi da Imani Sam Sam ɗari bisa ɗari sai yace La'ilaha Illallahu Muhammadur Rasulullah, yana mai Imani da wannan. Ya zama Mumini wanda yayi Imani da Manzo (S)
Ma'asumah Nigeria News Update
08132933333
Tags:
Taskar ilimi