Soyayyar Bayin Allah baza ta Taba Haduwa Data Makiya Allah Ba !!!


______Jibril Usman Sarki
Allah ta'ala a cikin Alkur'ani a Suratul Mujadala aya ta 22, yana cewa:

ﻻ ﺗَﺠِﺪُ ﻗَﻮْﻣﺎً ﻳُﺆْﻣِﻨُﻮﻥَ ﺑِﺎﻟﻠَّﻪِ ﻭَﺍﻟْﻴَﻮْﻡِ ﺍﻵْﺧِﺮِ ﻳُﻮﺍﺩُّﻭﻥَ ﻣَﻦْ ﺣَﺎﺩَّ ﺍﻟﻠَّﻪَ ﻭَﺭَﺳُﻮﻟَﻪُ ﻭَﻟَﻮْ ﻛﺎﻧُﻮﺍ ﺁﺑﺎﺀَﻫُﻢْ ﺃَﻭْ ﺃَﺑْﻨﺎﺀَﻫُﻢْ ﺃَﻭْ ﺇِﺧْﻮﺍﻧَﻬُﻢْ ﺃَﻭْ ﻋَﺸِﻴﺮَﺗَﻬُﻢْ

Ma'ana
Ba zaka sami Al'ummar da suke da Imani da Allah da Ranar Lahira suna soyayya ga wanda ya sabawa Allah da Manzon sa ba, koda sun ka sance iyaye ko 'ya'yan su, ko 'yan'uwan su ko kuma dangin su....
Yazo cikin ruwaya ingantacciya cikin littafin Almustarafaatus Sara'ir, Jildi na 3, shafi 640, na Babban Malamin Imamiyyah Sheikh Ja'afar Muhammad bin Mansoor bin Ahmad bin Idrisul Hilli, cewa:

ﻗﻴﻞ ﻟﻠﺼﺎﺩﻕ ‏( ﻉ ‏) : ﺇﻥّ ﻓﻼﻧﺎً ﻳﻮﺍﻟﻴﻜﻢ ﺇﻻ ﺃﻧﻪ ﻳﻀﻌﻒ ﻋﻦ ﺍﻟﺒﺮﺍﺀﺓ ﻣﻦ ﻋﺪﻭﻛﻢ ، ﻓﻘﺎﻝ : ﻛﺬﺏ ﻣَﻦ ﺍﺩّﻋﻰ ﻣﺤﺒﺘﻨﺎ ، ﻭﻟﻢ ﻳﺘﺒﺮﺃ ﻣﻦ ﻋﺪﻭﻧﺎ

Ma'ana
Ance da Imam Ja'afarus Sadiq (S.A): Wani Mutum na Maku biyayya sai dai yana da rauni wajan tawaye ga Makiyan ku! Sai Imam Sadiq (S.A) Yace: "Yayi karya duk wanda ke raya kaunar mu (Ahlul Baiti) baiyi tawaye ga Makiyin Mu ba."

A ayar farko da muka kawo cikin suratul Mujadala zamu iya fahimtar haramcin hada kaunar Makiya Allah da Masoyan sa, koda kuwa iyaye, 'ya'ya da dangi, sannan hadisin Imam Sadiq ya kara bayyana mana ma'anar ayar a fili inda ya karyata masu hada kaunar Ahlul baiti da Makiyan su. 
Wannan na nuna Bara'a (Tawaye ga Makiya Ahlul Baiti) da Wilaya (Mika wuya ga Ahlul Baiti) ne hakikanin Imani da Allah ta'ala.
A irin wadannan ranaku na Shahadar Wasiyin Manzon Allah Imam Ali (S.A) ya zama wajibi ga Muminai su maida alkalamin su wajan wayarwa da al'umma kai akan hakikanin Imani (Bara'a da Wulaya) domin Imamai Ma'asumai sun nuna mana muhimmancin bayyana tawaye da la'antar Makiyan su, kamar yadda yazo cikin littafin Imaratul Wulaya, shafi na 51, cewa:
ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﺧﻴﺎﻁ ﺑﻘﻤﻴﺼﻴﻦ ﺍﻟﻰ ﺍﻹﻣﺎﻡ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ‏( ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ‏) ﻗﺎﻝ : ﻋﻨﺪﻣﺎ ﻛﻨﺖ ﺃﺧﻴﻂ ﺃﺣﺪ ﺍﻟﻘﻤﻴﺼﻴﻦ، ﻛﻨﺖ ﺃﺻﻠﻲ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﻋﻨﺪﻣﺎ ﺃﺧﻴﻂ ﺍﻟﻘﻤﻴﺺ ﺍﻵﺧﺮ ﻛﻨﺖ ﺃﻟﻌﻦ ﺃﻋﺪﺍﺀ ﻣﺤﻤﺪ ﻭ ﺁﻝ ﻣﺤﻤﺪ ‏( ﻉ ‏) ، ﻓﺄﻱ ﺍﻟﻘﻤﻴﺼﻴﻦ ﺗﺨﺘﺎﺭﻩ؟ ﻓﺎﺧﺘﺎﺭ ﺍﻻﻣﺎﻡ ﺍﻟﺼﺎﺩﻕ ﻋﻠﻴﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ ﺍﻟﻘﻤﻴﺺ ﺍﻟﺬﻱ ﻛﺎﻥ ﺍﻟﺨﻴﺎﻁ ﻋﻨﺪ ﺧﻴﺎﻃﺘﻪ ﻳﻠﻌﻦ ﺃﻋﺪﺍﺋﻬﻢ ‏( ﻉ ‏) ﻓﻘﺎﻝ : ﺍﻧﻲ ﺃﺣﺐ ﻫﺬﺍ ﺍﻟﻘﻤﻴﺺ ﺃﻛﺜﺮ

Ma'ana
Wani Tela (Mai'dinki) yazo wajan Imam Sadiq (S.A) da 'dinkakkun riguna 2, yace da Imam: Lokacin da nake 'dinka daya daga cikin wadannan rigunan na kasance ina Salatin Annabi da Zuriyar Sa, haka kuma lokacin da nake dinka dayar na kasance ina tsinewa Makiya Muhammadu da Zuriyar Sa (S.A), A cikin rigunan 2, Wacce zaka zaba? Sai Imam Ja'afarus Sadiq (S.A) Ya zabi rigar da Tela ya 'dinka a yayin da yake Tsinewa Makiyan su (Ahlul Baiti), Imam Yace: "Nafi son wannan Rigar fiye da waccan."

Yaa Allah kayi Shaidar Mu, Munyi tawaye ga taron Saqeefa. wanda yayi sanadin Shahadar Ahlul Baiti da Masifun da Al'umma ke ciki a wannan Zamani!!
Sannan Muna tawassuli da rigar da aka 'dinka ta ana la'antar makiya Ahlul baiti, Allah ka kara dubun dubatan azaba ga Abdurrahaman bin Muljam Almuradi da ya sari Imam Ali (S.A) a goshi lokacin da take yake sujada.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post