#Bashir_Adam
•
1. Ki kiyayi Namijin da ba ta jin tsoron ubangijinsa.
2. Ki kiyayi Namijin da yake yawan baki manyan kudi, batare da kin buqata ba
3. Ki kiyayi Namijin da bai da ilimin Addini ko na zamani, musamman ma na addini
4. Ki kiyayi namijin da baya, yabonki akan dukkan koqarinki
5. Ki kiyayi namijin da yake fifita ilimin zamani akan na addini, wata rana zai ce kindamesa da karance_karance littafan addini
6. Ki kiyayi namijin da yake yawan raka samari hira da kuma yawan kiraye_kirayen 'yan mata
7. Ki guji namijin da yake yawan yabon wata, bayan antsayar da magana tsakaninki dashi, tabbas wataran zai canzaki
8. Kada kiyi gangancin Auren namijin da kawai iya gayunsa yake birgeki, aa 'yar uwata duba zuciyarsa, da dabi'ubsa
9. kiyi cikakken binciken mijin da zaki aura, har ta janibin abokansa
10. kiyi bincike cikakke akan iyayen wanda zaki aura, musamman sirikanki
11. Kiguji namijin da yake yawan kusantarki a lokutan hiranku
12. Ki guji Namijin da yake yawan miki wasu zantuka da suka sabawa tarbiyyar addini.
YA ALLAH KABAWA SISTOCINMU MAZAJE NAGARI MASU RIKO DA HARKA ISLAMIYYAH
Ma'asumah nigeria news updates