Shin, Da Gaske ne Wai Allah ya hana Annabi (S) Yin Addu'a Akan Azzalumai ??


Amsar Wannan na cikin Al'Qur'ani..

Za ka ji irin wadannan maganganu na fitowa daga bakunan wasu malamai, kuma har ana dogaro da wannan magana ta su wajen qalubalantar dukkan wanda aka ji shi yana yin addu'ar halaka ko lalacewar azzalumi.

su kan kafa hujja da cewa akwai wata rana Annabi (S.A.W.W) na yin addu'ar tsinuwa kan wasu mutane sai Allah ya hane shi, wai ba a yin addu'ar tsinuwa ga duk wani mai laifi matuqar musulmi ne, sai dai in ya kasance mushiriki. Ga dai hadisin kamar haka:-

Bukhari yace, Ahmad Bn Muhammad ya bamu labari, Abdullahi ya ba mu labari, Ma'amar ya bamu labari daga Zuhriy, daga Salim, daga Ibn Umar cewa ya ji Annabi (S.A.W.W)yana fada cikin sallah bayan ya dago daga ruku'u, yace;Allahumma Rabbana wa Lakal-hamdu fee akhereen !Sa'annan yace;

‘’ YAA ALLAH ! KA TSINEWA WANE DA WANE .‘’ Sai Allah ya saukar da;

‘’ BABU KOMAI A GARE KA GAME DA AL'AMARIN (shiriyar su), KO DAI ALLAH YA KARBI TUBARSU KO KUMA YA YI MUSU AZABA (babu ruwan ka), DOMIN SU AZZALUMAI NE ‘’. (Al-Imran:128)

(Bukhari, hadisi na 7346)

Tabbas, akwai shakku cijin wannan magana ta Ibn Umar, domin ta fi kama da cewa so ake yi a lullube miyagun ayyukan wasu ta hanyar nuna cewa Annabi (S.A.W.W)ya yi ba daidai ba.

Ga dai ayoyin da muka dogara da su wajen amsar wannan tambaya. Allah (T)na cewa;

‘’ TA YA YA MA ALLAH ZAI SHIRYAR DA MUTANE WADANDA SUKA KAFIRTA (ta hanyar qetare dokokinsa)BAYAN IMANIN SU, KUMA SUN YI SHAIDAR CEWA LALLE MANZO GASKIYA NE, KUMA HUJJOJI BAYYANANNU SUN JE MUSU? LALLE ALLAH BA YA SHIRYAR DA MUTANE AZZALUMAI. WADANNAN SAKAMAKINSU SHINE LALLE A KANSU AKWAI TSINUWAR ALLAH DA MALA'IKU DA MUTANE GABA 'DAYA. SUNA MASU DAWWAMA A CIKINTA (Wuta)BA A SAUQAQA AZABA GARE SU, KUMA BA SU ZAMA ANA YI MUSU JINKIRI BA.‘’

(Al-Imran, aya ta 86-88).

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 24th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post