Shin Alqunut sai a raka'a ta biyu ne kadai ake yinsa ?


TAMBAYA DA AMSA A BISA FIQIHU NA MAKARANTAR AHLULBAIT [A.S]

Tare Da Hujjatul Islami Walmuslimina Sheikh Ibrahim Abdullahi.

Tambaya: Shin Alqunut sai a raka'a ta biyu ne kadai ake yinsa ?

Amsa: Alqunut wanda yake na mustahabbi ne, wanda idan mutum ya yi, ya aikata abin da aka umurce shi da ya yi a matsayin mustahabbi, shi ne wannan qunuti da ake yi a raka'a ta biyu bayan fatiha da sura kafin a tafi ruku'u, wannan shi ne alkunutin da idan mutum ya yi, to ya aikata mustahabbin da aka ce a yi Alqunuti a sallah. Amma kamar yadda yake a Fiqihu na makarantar ahlulbaiti (a.s), mutum a kowane irin yanayi yake a cikin sallah, to yakan iya yin addu'a. 

Misali, idan mutum yana tsaye ko a raka'ar farko ne ya gama karatun sura ko fatiha, yana iya yin addu'a idan ya so, ko ya yi wani zikiri, amma amma ba da nufin cewa shi wannan zikirin ko wannan addu'ar da ya yi a matsayin crwa, an ce  masa ya yi wani abu ne na mustahabbi ne, a a, a matsayin ya halatta, a gareshi na ya yi wata addu'a, wacce ainahin ba zata rosa masa yanayin sallah din da yake ba, to babu matsala zai iya yin wannan abin, amma da nufin, cewa ita ce addu'a ko alkunutin da aka ce ya yi a cikin sallah, ba zai yi da wannan nufin ba, sai dai da nufin, ya halasta a gareshi ya yi.

         Daga, Zauren Al-ahkam.
Rbtw; Bilal Nasir Umar Sakkwato.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post