Sheikh Muhammad Turi a Shekaru 58 Masu Albarka.



     Daga -Idishia Jos. 

Muna masu godewa Allah da ya nuna mana wannan lokaci na farin ciki na shekaru 58 na Malam Muhammad Mahmoud Turi. Sheikh Turi bawan Allah ne muklisi wanda ya tsayu a turba na isar da sako na musulunci, Malam Turi ya samu kanshi cikin wanda suka amsa kira na maulana Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), wanda Shehu Usman Dan Fodiyo yayi bushara da zuwansa yake cewa yana daga cikin mataimaka na Imam Mahdi (ATFJ), har ma ya kara da cewa Shehu Akbar Ansarul Mahdi (ATFJ).

To, mutum ya tsinci kansa a wannan da'awa wannan babban daraja ne, babban baiwa ne da Allah (T) yawa shi Malam Turi. Malam Turi Allah ya mai baiwa a rayuwansa, idan ka dauki Malam Turi tun a tasowansa yake tare da Malam (H), kuma samartakansa gaba daya a wajen hidimtawa addini ne, rayuwan malam Turi misaline wanda kowa zai dauka ta fuskoki daban-daban. Idan ka dauki alakansa da ubangiji da alakansa da jagora da kuma sauran al'umma wannan ya isa mu dauki babban misali a rayuwan mu wanda zamuyi koyi dashi. Mu taru a waje daya ya isa ya nuna mana Allah (T) ya ainihin baiwa a Malam Turi.

Malam Turi rayuwansa abin koyi ne, rayuwan Malam Turi da alakansa da su Malam (H) shine shaksiyan Malam Turi yayi fana'i da shaksiyan su Malam (H). Babu wani abu da malam Turi zai yi wanda zai zama ba umarni ne na su Malam ba, babu wani abu da zaka ga yayi na sabawa su Malam a aiki ne ko a magana. Dan haka Malam Turi ya zamo 'Da na hakika mai sallamawa jagora wanda ya tsaya kyem wajen bin sahun jagora. Idan ka dauki janabin alakansa da 'yan uwa dukkan mu shaida ne yadda yake tafiyar da mutane daban-daban yadda yake nuna Kauna da soyayya ga dukkan wanda yazo gare shi.
Kyautatawan Malam Turi ga 'yan uwa da sauran mutane gari, ballan tana kazo wajen fagen jajircewa da istikamansa da sabaty. Malam Turi a wannan harka jajircecce ne, wanda ya zamo zargin mai zargi baya canza shi akan abinda yake akai, haka kuma barazanar mai barazana ba zai sa yayi rauni akan abinda yake akai ba. Ya sha jagorantar muzaharari wanda za'a bude wuta amma zaka ga Malam Turi baya ja da baya. Ya sha bayanin cewa babu wata uwa da zai sa yaji tsoransa in dai akan maddini ne.

Malam Turi baya tsoron duk wanda zai mishi wani abu Indai akan addini ne, ko kuma akan abinda ya shafi jagora, kuma ya zama misdakin na fadin Allah (T) da yayi; "Illallazina Kalu Rabbunallah Summas Takamu" don haka zaka ga shi Malam Turi yayi 'Istikama'. A tsawon lokaci ko a tsawon tarihi an yi fitintunu amma babu wata fitina da ta girgiza malam Turi ko ta raunana zuciyarsa ga jagora Sayyid Zakzaky (H). Don haka Malam Turi Allah ya mai baiwa mai yawan gaske don haka ya zame mana babban baiwa abin misali, domin yau a harka 'yan uwa suna da bukatan irin wannan.

Allah ya yiwa Malam Turi baiwa na Mukarimul Aklak, gaskiya, amana, alkawari, kyautatawa wajen mu'alama kyautatawa wajen magana abubuwa da daman gaske suna faruwa wanda zai sa Malam Turi yayi fushi, amma zaka ga ko yayi fushin ma in dare yayi zaka ga yana murshi to shikke nan wannan abin ya wuce. Duk yadda za'a bata mai rai in yayi murmushi to shikke nan  al'amarin ya wuce, zaka iya bata mai rai sai ya kyautata maka. Wannan kaga duk dabi'une da hali na su Malam (H), wanda zaka iya cewa sawu da kafa yana bin Malam da irin halayensa. Shi yasa kuma Allah ya daukaka darajansa da matsayinsa a cikin almajiransa gaba daya.

Rayuwan Malam Turi tana gudana ne akan nizami, tuntuni Allah ya mai wannan baiwa yana da lokacin ibada da karatun Alkur'ani da askar, sannan da lokacin ganawa da 'yan uwa, sannan da lokacin da yake hutawa. Malam Turi bai cika magana ba, sannan yana da kawaici, yana da yawan shiru, idan kaga yana magana to akan abinda ya shafi addini ne ko akan abinda ya shafi wannan harka ne. Malam Turi yana bin sayyid sau da kafa a tsawon tarihin harkan nan zan iya cewa ban san wani daga cikin Almajiran Malam (H) da ya aiko da sako na musamman yana cewa idan 'dan uwa yana tare dashi to, kada ya zartar da wani abu har sai ya shawarci Malam Turi. 

Sayyid ya ambaci Malam Turi a matsayin jagora, "Allahumma salli ala Muhammad " sabida komai yana tafiya cikin jagoranci, tun daga wannan lokacin duk wani abu da dan uwa zai yi zai zo ya tuntubi Malam Turi. Lokacin da Malam ya kawo Malam Turi Kano cewa yayi ga Idon mu nan! Wannan ya isa ya zama babban ishara na girma da kususiyya na su Malam Turi a wajen su Malam. Don haka abinda yake garemu, mu a yanzu abinda yake gaban mu da irin tarbiya da halaye da dabi'u da sadaukarwa shine irin sadaukarwa Malam Turi. Mu zamewa Malam a rayuwan mu kamar yadda Malam Turi ya zama wa Malam (H) a rayuwan shi. Wanda ya zamo cewa gaba ki daya rayuwan shi sallamawa addini ne da taimakawa jagora.

Kowa da kowa na Malam Turi ne, wajen Mu"amala malam Turi yana tafiya da kowa da kowa ba tare da cewa kana son shi ko baka son shi ba. Yana mu'amala da kowa ne. Dan haka kowa nashi ne, Malam Turi Yasha wahalhalu da jarrabawa amma ya nuna juriya da hakuri, Malam Turi irin juriyansu sai waliyan Allah. Babu wani wanda zai munana Malam Turi face Malam Turi bai kyautata mishi ba, kuma babu wani wanda zai zo da damuwa ba tare da Malam Turi ya biya mai bukatansa ba kuma batare da wani ya sani ba. Dabi'unsa abin koyi ne, dabi'unsa ya samu ne daga su Malam (H).

To, Mai karatu anan zan tsaya sabida gudun tsawaita rubutun ga masu karatu. Daga alkalamin --Idishia Jos. 

#FreeZakzaky

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post