_inji Jagoran gaskiya
"Wani ‘Clip’ da ake ta yawo da shi na hirar Wisal, suka ce; abin da ban tsoro cikin jihohi hudu kawai, an samu mutum Miliyan Ashirin da Biyar, abin da ban tsoro, ya ce; to mene abin yi? Cikin abin da suka ce har da cewa ainihin an yi hira da shi Al-Zakzaky, Zakzaky (wani mutum ne sunan shi Zakzaky), to shi Zakzaky din nan wata jarida ta Kuwait ta yi hira da shi ya ce; ayyukan da wadannan ‘yan ta’adda suke yi da sunan sunnah, ya fi taimakon mu fiye da wa’azin Malaman Shi’a, suka ce; wadannan ‘yan ta’addan ba su san barnar da suke ma sunnah bane? To, yanzu kuma abin mamaki don dodewar basira yanzu kuma za su ba da kudi a yi ta’adda da sunan sunnah, to kuma zai da kara bude ido.
Mu a wurinmu, kamar yadda Imam Husain yake tare da Sahabbai, wadanda ya ce bai ga Sahabbai kamar Sahabbansa ba, irin wadannan Hilal bn Nafi’I din nan, irin wanda suka ce yi damu Gabas ko Yamma duk inda ka yi muna tare da kai, muna bisa basira kan cewa muna tare da gaskiya ne.
To, irin wannan ne zamu dake, ‘thaura’ din Imam Husain abin da ta koyar ke nan. Nasara ta wata hanya da ba a tsammani, su suna tsammanin da karfin tsiya ne da haukataku da makamai da shi ake nasara, ‘billahi alaikum’, idan mutum yana da hankali ya duba ya gani, saboda Allah makami aka sa aka tara mutanen da kuke gani? Fada aka yi? Zagi aka yi? Hankali da ilimi, to, amma kuma me ya tattara wannan? Jinin Imam Husain da jinainan iyalan gidansa da Sahabbansa, shi ya tattara mana mutane, yanzu kuma sai ana mana barazanar za a shekar da jini, ‘billahi alaikum’, wanda yake ganin shi ba zai ba da jininsa ba, to dama ya ja baya."
***
- Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) a taron rufe zaman juyayin ashura na bana. 1437-2015.
Auwal Yusuf Muhammad