Take Hakkin Dan Adam Ranar 12-12-2015 Zuwa 15-12-2016
DAGA SHAFIN 🌍MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES
__________________↓ ↓ ↓ ↓
*Tare da Wakilinmu Aliy Haidar Lawal Tudun Iya +22963184499*
•
HAKIKA WANNAN RANA TA ZAMA RANA MAI TARIN BABBAN TARIHI A IDON DUNIYA A INDA AKA TAKE HAKKIN DAN ADAM DA TSANTSAR ZALUNCI ACIKI.
Ina son yin magana akan abun daya faru ranar atakaice.
1-take HAKKIN Dan Adam afuskacin hankali
Koba komai ace mutum baisan Allah ba baiyarda da kiyamaba. Yasan cewa ZALINCI ba abu bane mai kyau kuma duk wani dan Adam yasan dan Adam Dan uwansa Yana da kima da daraja.
Ranar 12 GA watan 12 inyi mummunan cin zarafi GA mabiya mazhabar shi'a a ZARIYA wanda masu hankali suke tanbaya laifin me sukai?. Zan iya cewa ko'a jahiliya basu yadda da kisan yara da mata ba a filin yaki harda ma tsofaffi da wanda baizo dan yaki ba.
Amma a wanan ranar ankashe yaro an kashe tsofo an kashe mata an kashe mai ciki abisa tabbataccen zalinci wanda duk wani Dan Adam zaiyi Allah wadai da abun da akai. Abun mamaki shi ne hukuma tai wannan aika aika. Abun tashin hankali da tausayi shi ne yadda aka kona mutane da ransu aka dau wadanda aka kashe aka binne a rami daya wanda babu wani mai hankali dazai yadda da hakan. Kuma karin zalinci ankama jagoransu antsareshi abisa zalinci tare damai dakin sa da daruruwan mabiyansa
Wanda babu wani hankali komai hankali dazai yadda da hakan indai yasan darajar dan adan.
2 nazari akan sharia
*
Wanda wannan danyan aikin babu wata shari'a ta musulunci kota kafirci data yadda da wanan aikin
Anfake da cewa sunyi laifi
Mun yarda cewa sunyi laifi
To ayanke masu hukunci mana
Tunda muna da kundun tsarin mulki na kasarmu Nigeria
Insun tare hanya amasu hukuncin tare hanya in sunyi kisa a masu hukuncin kisa mana yadda sharia ta tanada mana.
Wannan aiki da sojojin Nigeria sukai ya saba ma shariar kasarmu
Dan haka bama goyan baya, zaluncine kuma take hakkin dan adam ne.
Muna bukatar ayi masu adalci suma yan kasane
Bugu da kari tsarin mulkin kasata Nigeria yaba kowa damar yayi addini yadda ya fahimta kuma ya yadashi. Me yasa ake tauye masu wannan hakkin nasu?
Muna fatan masu hankali zasu duba wannan matsalar kuma susa baki wajen yima wadannan bayin Allah adalci
.
Tammat bi hamdulillah
_*Daga Wakilinmu 🌍Ma'asumiya Nigeria News Updates*_