Nifa Ranar Jumu'a Zan mutu...!!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MARIGAYI AHMAD HARUNA JIBRIL GUDA

Yaro ne mai yawan fara'a tare da girmama duk wanda ya san yana sama da shi a haife, har ma na qasa da shi yakan dauke su tankar abokansa ne.

Ba shi da abokin jayayya ballantana ace an tabs ganinsa ya yi fada da wani ko kuma a kawo qararsa kan cewa ya yiwa wani abinda ba daidai ba.

Yaro ne da yayi karatun ilimin kiwon lafiya kamar yadda mahaifinsa yayi, kuma yana taimako sosai wajen kula da jinyoyin jama'a, musamman ma mazauna qauyen garin Guda dake qaranar hukumar Ningi ta jihar Bauchi.

Bai wuce saura kwana 50 ba yayi aure Allah ya karbi kayansa.

ISHARORI KAFIN MUTUWARSA
____________________________

- Ya kaiwa wata mata dinkin wani kaya sai take ce masa Ango ! Sai ya bude baki yace mata;

‘’ WA YAKE BATUN AURE KUMA? AI MU DA AUREN SAI A ALJANNAH, MATANMU NA CAN !‘’

- Wani ya gan shi da sabbin kaya a jikinsa shine yake ce masa, kai fa ksna samun sabbin kaya za a gansu a jikinka. Sai yace;

‘’ TO, MEYE DUNIYAR NE? ITA MUTUWA ZUWA TAKE MAKA BA SAI KA SHIRYA MATA KO TA SA MAKA RANA BA !‘’

- Wata rana kuma yake cewa;

‘’ NI FA RANAR JUMA'A ZAN MUTU .‘’

Kuma a irin wannan rana juma'a 22nd November, 2019 ya rasu bayan sallar magrib.

- Cikin fara'a yake cewa wani, ‘’ IDAN NA MUTU ZA KU SHA MAMAKI WAJEN GANIN YAWAN JAMA'A .‘’

Na sha halartar jana'iza a cikin garin Ningi, amma wallahi ban taba ganin yawan jama'a kama tasa jana'izar ba, da kuma zunzurutun matasa.

Ya rasu ya bar 'ya guda daya (1)da kuma Uwa da Uba.

AHMAD, ALLAH YA KAI RAHMA QABARINKA ALBARKACIN ASALIN MAI SUNANKA (S.A.W.W).

YA SA ALJANNAH CE MAKOMARKA TARE DA BAWA MAHAIFANKA DA 'YAN'UWANKA HAQURIN WANNAN RASHI DA SU KA YI. YA KUMA RAYA MAKA 'YARKA WACCE KA BARI TARE DA CIKAWA DA IMANI YAYIN KOMAWARTA GA UBANGIJINTA.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

       08126385470

~ 24th November, 2019.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post