NA SAMU KARFIN GUIWA WAJEN IBADA DA SANIN HARKA A WAJEN SHEIKH TURI.

Malama Jamila Muktar Sahabi Kaduna ke jawabi a wajen taron Bikin cika shekaru 58 na Malam Turi a Kano.


--Idishia Jos.

"Na tuna wani abu wanda yake min tasiri musamman akan abinda ya shafi 'ya'yan mu a lokacin haihuwan Ukasha Malam Turi ya aiko yace a fada min daga cikin hakkokin 'ya'ya akan mahaifiyarsa a lokacin da zata haifeshi ta tabbatar cewa wacce zata karbi haihuwan macece mumina kuma ya kara da cewa ta fada min koda haihuwan ya zo ta daure aje asibiti. Haka kuma Alhamdulillah da haihuwan yazo da ita Malama Maimuna da wata sister suka karbi wannan  Haihuwan Ukasha a Ramadan.

Tasirin wannan a fada maka abu ma tun kafin ya sameka, da kuma mahimmancin su da fa'idansa sai ya zama yamin tasiri a dukkan Haihuwan da zan yi. Zama na dasu Sheikh Turi lokacin da muka yi aure da Malam Muktar ban gama Sekandiri ba cewa tunda makarantun Gwamnati ana samun matsalan Hijabi to a mai dani wata makaranta a nan Kaduna. A lokacin da Malam Muktar zai tafi Sudan Malam Turi yace min kada ki damu kin ga yanzu in muka tafi ke kadai zaki zauna daga ke sai 'ya'yanki Ukasha da Asma'u, kina da lokacin da zakiti karatu.

Kinga Malam Muktar zai tafi karatu to, kema anan yanzu ki dage ki bada kokari wajen yin karatu. Don haka karatu na ya samu asali ne da taimako na Malam Turi. Sannan a lokacin da muke zaune ita Malama Maimuna ta kasance tana karantar da matan Anguwa, akwai matan Anguwa da suke zuwa tana karantar dasu. Lokacin da Malam Turi yake zuwa karatu Zariya zai tafi ranar Asabar da safe ya dawo Laraba, to har muna murna ya dawo in yazo ranar Laraba ya iso da safe saboda kyautan da zai ma wadan nan matan da suke karatu da Malam Maimuna domin ya shajja'asu.

Haka bangaren ibada na samu  karfin gwuwan yin ibada saboda inuwar Sheikh Turi da nake hangowa daga cikin window dakin sa. Lokaci Karfe 2 daidai in dai zaka fito tsakar gida zakaga inuwar Malam Turi yana Ruku'u yana Sujjada, wani lokacin zaka ga inuwar Malama Maimuna a bayansa tana bin sa Sallah a daidai wannan lokacin. Wani abu da zan kara fada shine akwai lokaci nasan 'yan uwa da yawa sun san wannan magana da Malam Turi yayi yake cewa 'ko mutuwa bata isa ta raba shi da sayyid ba'. Lokacin da ya fadi wannan magana da muka koma gida sai nake fadawa Malam Muktar cewa kaji wani magana da Malam Turi yake cewa."

Daga Shafin Ma'asumah Nigerian News Update.

  -daga jawabin Malama Jamila Muktar sahabi a wajen taron Birthday Sheikh Muhammad Turi a Markazin 'yan uwa dake Kano kofar waika.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post