SUNNAR ALLAH BA TA CANZAWA
Qur'ani littafi ne da ke dauke da tarihin magabata, ya tattara dukkan abubuwan da suka auku domin mu kasance masu daukar darasi daga gare shi. Sannan kuma a cikinsa akwai umarni da hani, wadanda ake so mu kiyaye domin neman samun yardar Allah.
Daga cikin abinda Qur'ani yazo mana da shi akwai qissar Fir'auna da Musa (A S), wanda ya kasance ya zo daidai a wannan zamani na mulkin Fir'auna Buhari da Musan zamaninsa Sayyid Zakzaky (H).
KU BIYO MU
" KUMA MASHAWARTA DAGA MUTANEN FIR'AUNA SUKA CE; " SHIN, ZA KA BAR MUSA DA MUTANENSA, DOMIN SUYI BARNA A CIKIN QASA, KUMA SU BARKA KAI DA GUMAKANKA?" YACE; " ZA MU YANYANKA 'DIYANSU MAZA KUMA MU RAYA MATANSU, KUMA LALLE NE MU A BISA GARE SU MARINJAYA NE."
Irin wannan magana mutane ke fadawa Buhari game da Sayyid Zakzaky (H) da mabiyansa, kuma ya dau aikin da kakansa Fir'auna yayi na kashe mutane.
" MUSA YA CEWA MUTANENSA! " KU NEMI TAIMAKO (addu'a) DA ALLAH, KUMA KUYI HAQURI, LALLE NE QASA TA ALLAH CE (ba ta Fir'auna ba), YANA GADAR DA ITA GA WANDA YAKE SO DAGA BAYINSA, KUMA AQIBA TA MASU TAQAWA CE."
" SUKA CE; " AN CUTAR DAMU DAGA GABANIN KA ZO MANA, KUMA DAGA BAYA DA KAZO MANA." YACE; " AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINKU YA HALAKA MAQIYANKU, KUMA YA SANYA KU KU MAYE A CIKIN QASA, SA'AN NAN YA DUBA YADDA KUKE AIKATAWA."
" KUMA HAQIQA MUN KAMA MUTANEN FIR'AUNA DA TSANANIN SHEKARU (na fari) DA NAQASA DAGA 'YA'YAN ITACE, TSAMMANINSU SUNA TUNAWA (amma a banza) ."
" SA'AN NAN IDAN WANI ALHERI YA JE MUSU SAI SUCE; " WANNAN NAMU NE ", KUMA IDAN MASIFA TA SAME SU SAI SUYI SHU'UMCI DA MUSA DA WANDA YAKE TARE DA SHI. TO, SHU'UMCINSU A WAJEN ALLAH YAKE, SAI DAI MAFI YAWANSU BA SU SANI BA."
(A'araf:127-131)
Kuyi nazari da kyau, irin halin da muke ciki kenan yanzu.
DANNA NAN: -Ma`asumah Nigeria 🇳🇬 news 📰 update domin kasancewa damu a Facebook.
Tare da Ado Isah Guda
08126385470-08137925034