Jawabin Jagoran gaskiya [sayyid zakzaky]
Mu nan (duniya) kam halitta ba ta da dangantaka da aikinka, baiwa ce ta
Allah. In Allah ya yi ka ko ma yaya ne, ka gode wa Allah yadda ya yi
ka. In ma kai a ganinka ma da ya yo ka ba ka da rabo na kyau mai yawa,
don kowa yana da rabonsa. Don dan Adam Allah Ta’ala ya yi masa
kyau. Inda mutum zai san Allah ya yi masa kyau, ya duba sauran halitta
ya gani. Ko dan Adam yana jin haushin wata halitta? Ko da Mariri ne ko
Barewa? Yanzu za ka ga wata 'yar Barewa ka ce ina ma kai ne 'yar
Barewar nan saboda ta cika kyau? Ba wata halittar da ta yi kyawun dan
Adam.
Kuma mu ma din a cikin halittar nau'in mutum, an nuna cewa mune na
qarshe, don akwai wadansu mutane da aka yi kafin mu wadanda suka
zauni wannan doron qasa din. Yanzu binciken zamani ma ya kai ana ta
ciro qasusuwa, da yake ilimi na dan Adam na yanzu ya sa in ya ciro
qashi yana iya mai da sifar mutumin a gane. In an mai da siffar sai a ga
mutumin bai kama da bil Adaman yanzu ba. Yana da wata siffa wata iri
Su ma mutane ne, amma ba su yi kama da 'yan adam ba. Wasu suna da
girman jiki, wasu manya-manya ne wasu 'yan qanana ne, wasu kuma
siffar ta dan bambanta da Biri kadan ne. Ga su nan dai haka nan.
Shi dan Adam shi ne aka yi a mafi kyakkyawar kama "Laqad
Khalaqanal Insana fi Ahsani Taqwim." Mun halicci mutum a mafi
kyawun matsayi a daidaito, wani ba zai iya tunanin yadda ya kamata a yi
mutum kamar yadda Allah ya yi shi ba, wannan baiwa ce tasa wadda ya
yi mana. Muna godiya gare shi kan wannan. To ko ya ya yi maka
wannan baiwar, sai ka gode wa Allah. Kuma in ma kana ganin wasu a
halitta sun fi ka kyau, to ka dubi kai kuma wadanda ka fi. Akwai
wadanda ka fi da yawa.
Saboda haka wannan a taqaice abin da nake cewa, wannan baiwar Allah
ce wadda ya riga ya bayar. To amma gobe qiyama abin zai bambanta.
Wannan baiwarsa ce, amma kai kuma an ba ka daman ka bayar da
gudummawa ga yadda kake son ka kasance. Ka ga sai ya zama halittarka
ta gobe qiyama kai ma kana da hannu a ciki.
Yanzu da za a ce an bayar da dama kowa ya zabi yadda yake so, ya kuke
tsammani? Ban ce kai ka yi kanka ba, in kai za ka yi kanka za ka
yamutsa lamari. Kamar a ba ka wadan su samfurori. A jera wadansu samfurori a ce to zabi daya, ka san kowa zai darje ne ko? Zai darje
wanda ya fi kyau ne. To yanzu ga daman an riga an ba mu. An ce yanzu
mu kyautata dabi'unmu gobe qiyama mu zama kyawawa a halitta. Ba ka
ga kamar an gina 'Model' ba, to ga 'Model' nan, ga bayin Allah na
gargaru nan, wanda aka ce ka yi koyi da su. Kowace 'Hasala' ta kirki sai
ka sami wani ya yi 'Zarra' a kanta.
*©Mahadi Tukur Almizan*
[ TASIRIN DABI'U ]