JAWABIN SHEIK YAQUB YAHAYA A MAKON HADINKAI KATSINA, Rana ta 03).
🇳🇬Ma'asuma Nigeria News Update, tare da Isma'il Abubakar Idris Katsina
Sheik Yaqub Yahaya yayi wasu guntayen Jawabai a wajen taron Makon Hadin kai bayan Sheik adamu Tsohonya safka daga bisa munbarin Jawabi a Filin Tanki Rafin Dadi cikin garin Katsina.
Sheik Yaqub yace yahudawa sunce "Zamu kirkiri wasu mutane wadanda zasuji komi sukayi dai-dai ne a cikin Musulmai, zamu kafa kwamnati mu gallazama mutane mu yada barna a cikinsu sai munga mutum ya kure wajen Zalunci da barna da lalacewa, kwalkwadon lalacewar mutum kwalkwadon mulkinda zamu bashi, tamkar yadda suka nada Buhari inji yahudawa".
Mulkin buhari dai-dai yake da mulkin da akayi na kisa da zalunci a shekara ta 1991 Aljeriya da Saudiyya tarika taimaka Yahudawa da makamai.
Sheik Yaqub Yahaya wajen Makon Hadin kai rana ta (03) a Filin Tankin Rafin dadi bayan Malam Adamu Tsoho Jos ya safka daga Munbari.