Mu Da Muka Yi Imani Da Wannan Harkar Ne Za Mu Tallafa Mata


Daga Bilal Nasir Umar Sakkwato

An yi kira na musamman ga ƴan uwa da su duƙufa gurin cigaba da bayar da gudummuwa da duk abin da suke iyawa ga wannan Harka. Shekh Sidi Munir ne ya yi wannan kiran a daidai lokacin da yake gabatar da jawabi a gurin walimar maulidin Hatama wanda ƴan uwa musulmi na Da'irar Sakkwato suka gabatar, yake cewa;

“Muna jin abubuwan da suke faruwa a Abuja kwanan nan, azzalumai sun dage sai sun ga bayan ƴan uwan da suke Abuja, waɗanda suke motsi akan Malam (H) ta hanyar buɗe wuta yayin da suka fito muzahara, saboda haka akwai buƙatar ƴan uwa mu sani mu kuma yi haƙuri, dole sai da namu kuzari na duk abin da muka iya ne sannan Allah (T) zai ƙare wannan jarabawa. Tun da aka je har gida aka yi harbi ga jikin su Malam mai albarka aka harbi iyalinsa, to mu sani ba haka kawai wannan jarabawar zata ƙare ba. 

A saboda haka muke ƙara kira tare da ƙarfafa ƴan uwa da cewa mu shirya mu nufi Abuja, wallahi nakan ji kunya sosai a duk lokacin da na ga hotunan yadda muke gudanar da taruka yayin bukukuwanmu, gamunan da yawa fululu amma mun bar ƙalilan da fafutikar nemawa jagora ƴanci.”

Haka kuma Malamin ya yi kira ga ƴan uwa dangane da biyan haƙƙin shuhada, ciki har da bayani akan Fom na Naira Miliyan ɗaya da rabi da Mu'assatus Shuhada ta fitar wanda suka buƙaci wannan yankin na Sakkwato da ya haɗa da Kebbi da Zamfara ya kasance sun yi biya domin tallafawa Mu'assasar. Haka kuma ya yi kira ga ƴan uwa domin tallafawa Abuja Struggle.

A ƙarshe Sheikh Sidi Munir ya ƙarƙare da baiwa ƴan uwa haƙuri da cewa, “Mu yi haƙuri mu kuma daure mu da muka yi imani da wannan Harka mune dai kuma za mu tallafa mata”.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post