Karanta kaji dalilin da yasa 'yan Shi'a basu da masallaci na kan su.
Masallaci Wajen Hada Kan Al'umma ne.
Shi masallaci kamar yanda muka sani waje ne na gudanar da ibada, amma kuma babban maqasudin hada al'umma a masallaci domin samun hadin kan su ne. Wannan yana daga cikin dalilan da yasa 'yan Shi'a basu da masallatai kamar yanda sauran akidu suke da nasu masallatan. Domin idan dai kowa zai bude masallacin sa daban to wannan zai zama ya raba kan al'umma ne.
Allah (S) ya samar mana da yanda zamu hada kan mu tun daga matakin Unguwanni, garuruwa, yankuna, da ma gurin da zai hada kan al'ummar duniyar dukkan ta. Idan yau aje masallaci kowa yana ganin kowa suna fahimtar junan su, a haka hadin kai zai samu.
DALILIN SAMAR DA MASALLACI:
1. An samar mana da masallatan unguwanni ne saboda Allah madaukakin sarki yana son yaga kan al'ummar Unguwan ya hadu. Amma yanzu a Unguwan guda sai a sami masallatai goma ko fiye da haka.
2. An samar da masallacin Juma'a ne saboda kan al'ummar gari ya hadu, kuma a kowane gari masallaci guda daya (1) ake bukata saboda duk wanda yake garin nan zai je yayi sallah ranar Juma'a. Amma yau a gari daya sai a sami masallatan Juma'a fiye da biyar.
3. Sannan an samar mana da masallacin Idi shi kuma an samar da shi ne saboda kan al'ummar yanki ya hadu. Misali kamar a local gov't sai a samu masallaci guda daya. Wannan shi kuma zai hada kan al'ummar yankin ne duka. Amma yau a gari daya sai a samu masallacin Idi fiye da daya.
4. Sai kuma aka samar mana da muhallin da zai hada kan al'ummar musulmi dukkan su wato masallacin dake Makkah kasar Saudi Arabia. Shi kuma masallacin an samar dashi ne saboda kan al'ummar musulmin duniya ya hadu. Wannan shi kuma har yanxu ba'a samu na biyun shi ba.
Wannan dalilan yasa 'yan uwa musulmi almajiran Sheikh Zakzaky (H) basu da wani masallaci nasu, sabo shi Malam Zakzaky (H) mai kira ga hadin kai ne da kuma zaman lafiya. Mun godewa Allah muna gabatar da sallah a kowane masallaci.
Ma'asumiya yau kinyi kuskure, 'yan shi'a suna da masallatai, idan Nigeria muke magana Suna dashi a Kano, Kaduna, katsina, Azare, yobe da Gombe, wannan wadanda ni na sani kenan, ta iya yiwuwa suna dashi a wasu wuraren na daban wanda bansani ba, kuma Mu'assasar 'yan shi'a ta RAAF ita ta Samar dasu.
ReplyDeleteMa'asumiya yau kinyi kuskure, 'yan shi'a suna da masallatai, idan Nigeria muke magana Suna dashi a Kano, Kaduna, katsina, Azare, yobe da Gombe, wannan wadanda ni na sani kenan, ta iya yiwuwa suna dashi a wasu wuraren na daban wanda bansani ba, kuma Mu'assasar 'yan shi'a ta RAAF ita ta Samar dasu.
ReplyDelete