kuzo kuji......
_Daga Shafin Ma'asumiya Nig News Updates._
*Tare da..... Journalist Daddy*
*_Na'am, ba zanyi mamaki ba kawai don naji wadannan zantuka mafi zurfi a jahilci da rashin sanin ya kamata ba daga kazamin baki murakkab…_*
_Magana mafi sauki wurin fahimta kwara daya tall kawai itace; "Shifa dan Adam mutum ne mai masifar kiyayya, gaba tattare da tsana izuwa ga abinda ya jahilta", a bayyane take, an bishe hasken da ambato tare da darajoji na iyalan annabi bisa son rai da zalunci tattare kiyayya mai dogon tarihi._
*_Bazan mance ba, daga cikin wadanda suka jahilci al'amarin Annabin Rahma kwatankwacin na Salafawan nan, suna zane a mafi munin kama tare da ishara da cewa wannan shine annabin rahma, sun dade suna aibatawa tare da bata Shaksiyyar annabim ta kowace fuska, amma abin lura anan shine; sufa masu wannan aikin na batawa tare da zagin Annbin Allah ta hanyar da duk suka ga dama wadda ya hada da jahudawa da wadanda ba sai na ambace su ba, suna hakan ne a bisa sun jahilci waye annabin hakikatan, tun farko balle ma su san hadarin da ke tattare da matakin zagi da suke dauka ba na jahilci akansa, da zasu zama masu imani tare da sanin wayen hakikanin annabi Muhammadu (sawa), da sun rika kuka mai tsanani sabida tuna irin tabargazar da suka tafka a baya har izuwa karshen rayuwarsu._*
_Irin wannanm misali sak shine misalin da zan Bayar a game da salafawa masu zagi tattare da assasa tsana a zukatan almajiransu a game da al'amarin Imam Mahdi (AF).
Idan Baku San imam mahdi ba, to bari kuji salsala da nasabar Imam mahdi jikan annabi._
*_Annabi Muhammadu (sawa) mahaifin Fadima._*
_Fadima Mahaifiyar Hassan da Hussain._
*_Hussaini mahaifin Aliyu Zainul Abideen._*
_Aliyu Zainul Abideen mahaifin Muhammad Baqir._
*_Muhammad Baqir mahaifin imam. Ja'afarus Sadiq._*
_Ja'afaru Sadiq mahaifin Musal Kazim._
*_Musal Kazim mahaifin Muhammad Ridha._*
_Muhammad Ridha mahaifin Muhammad Jawwad._
*_Muhammad Jawwad mahaifin Aliyul Hadi._*
_Aliyul Hadi mahaifin Hasanul Askari._
*_Hasanul Askari mahaifin Imam Qaimul Muntarzar, Muhammad Al~Mahdi._*
_Wannan shine Nasabar Imam Mahdi, idanfa kuka lura;shifa jikan annabi ne, yana daya daga cikin ma'asumai abisa i'itiqadin mu Shi'eey._
*_Amma abin tambaya shine; Meyasa Salafawa Izalawa suke zagin Imamu Mahdi tare da kiransa Shaidani?? Anya ba yahudawa sukewa aiki ba? Ko sun manta jikan annabi ne shi??? Sannan daga baya suyi ta babatun karya da cewa muna zagin Sahabbai, Lallai muna kwatanta masu zagin Imam Mahdi da suke yi izuwa ga masu zagin annabi bisa jahiltar waye annabin, domin da sun san girma da darajar Annabi Muhammadu (sawa), da sun tuke rayuwarsu a kuka da jimamin tabargazarsu. Haka suma salafawa, basu san waye Imamu mahdi ba, shiyasa har suke iya kushe shi, tare da danganta shi a kama mafi sharri (waiyazubillahi)._*
_Bisa dogaro da wannan dan karamin tsokaci, insha Allahu zan dakata ba don na gama ba, sai don ita rubutu taqaitacciya tafi mai yawa mare amfani._
*Daga; Almajirinku...... Journalist Daddy*