Daga;Journalist Daddy
Tare da
Masu'ud Dan Masani Shinkafi
A sau da yawa zaka ji Mutanen Ibo wanda Hausawa ke kira da inyamurai zaka ji suna kiran Hausawa da wani suna wai; "Aboki", har ma sun yi wani waka wai shi (Aboki shine my shoe) .
Zagi ne ko yabo????
Kuma wa ke zagin wani a cikin bahaushe da Ibo????
Dangane da kalmar Aboki, a can yankin Ibo, suna da wani shashashan dabba mai dabi'ar wawaye, gaba daya dai wannan dabban mare hankali ne a cikin dabbobi, kuma sannan sunan wannan dabban shine (Aboki) a yaren nasu na Ibo, so sai ya zamana Mutanen Ibo sau da yawa zaka ji suna kiran hausawa da wannan suna na (Aboki),
Da wani dalili suke danganta wannan sunan ga hausawa?
Kuma me yasa hausawan suke kiran Ibo da Inyamuri??
A lokacin da hausawa suka Matsawa Ibo lamba a lokacin yakin biafra, Mutanen Ibo sun sha wuya a hannun hausawa kwarai, ga yunwa, kishi, so sai ya zamana idan suka ga bahaushe yana shan ruwa a lokacin, idan suna bukata sai suce; NYA MIRI, kalmar farko na NYA, yana nufin (bani) na biyu kuma wato; MIRI, yana nufin Ruwa, idan ka hada wadannan kalmar duka wato NYA MIRI wadda take nufin bani ruwa kalmace ta Ibo, wadda take alamta bukatar ruwa a lokacin da suke cikin kaskanci.
To sai Malam bahaushe ya dauki wannan kalmar NYA MIRI, yace INYAMIRI, sai ya zamana kalmar ta yadu kwarai, har ta kai ga, idan ba ka cewa bahaushe Inyamiri ba, to bazai fahimce ka ba har ya zuwa wannan zamani namu. Wannan kalma ta Inyamiri tana masifar bakantawa Mutanen Ibo rai sosai, hakan ya sanya suma suke kiran Hausawa da wannan suna ta ABOKI, wadda hakan ke nufin wani dabba mummuna mai dabi'ar wawanci.
KARANTA WANNAN:- Tasirin karanta Tarihin Manzon Allah a Zukatan Muminai
A tawa fahimtar, a matsayina na dan shi'a, ina mai kira ga su Hausawa da su yi hakuri su daina kiran wadannan Mutanen da Inyamirai, su ma Mutanen Ibo su taimaka su daina kiran hausawa da suna Aboki. Domin Mu jagoranmu Sheikh Zakzaky ya koya mana zama da Mutane.
Illahy ya kubutar Mana Dashi bihakki fateemah Ma'asumah (s.a)
Illahy ya kubutar Mana Dashi bihakki fateemah Ma'asumah (s.a)
Tags:
Tunatarwa