Masu Kyawawan Ayyuka Zasu Zama Kyawawa, Masu Munanan Ayyuka Za su Zama Munana !!!


Inji Jagoran gaskiya* *[sayyid zakzaky*

Na'am, a nan Allah ya yi mana halitta yadda ya so, shi ya ba mu siffofinmu, yadda duk muka ga kanmu haka Allah ya yi mu, haka Allah ya ga daman yi. To amma gobe qiyama Allah zai canza mana halitta, zai ba mu wata siffa, za ta yi kama da tamu din nan, amma kuma za ka sami tasirin ayyukanmu bayyane a cikin siffofinmu. Masu kyawawan ayyuka za su zama kyawawa, masu munanan ayyuka za su zama munana.

A nan nakan ga masu zane sukan yi wani abu, kun san wani abu da ake ce wa 'Catoon', a jarida akan zana abu kamar wata halitta ta daban. Wato abin da mai zanen yake nufi, yana nufin ya nuna mummunar dabi'ar mutumin da ya zana din ne. Za ka ga wadansu mutane suna yin wannan irin 'Catoon' din. Akan nuna wani a talabijin, wani akan sa a jarida. 

Da ma galiba a jaridu aka fi zanawa. Sai ka ga sun yi mutum sun kamanta
shi da wani abu. Alal misali na tava ganin an kamanta wasu mutane guda biyu, daya aka yi masa qoqon Kunkuru a baya, daya kuma aka yi masa katantanwar Dodon Kodi a bayansa. Sai aka nuna shi Kunkurun
shi ne shugaban qasa, Dodon Kodin kuma shi ne mataimakinsa. Sai ana
cewa yana ce masa "ka yiwo sauri tafiyar fa na da nisa."` Wato suna
nufin cewa su waDannan mutane suna tafiya diqin-diqin, wato sun qi su
yi tafiya. Amma in ka gani za ka gane su sosai. Da ganin hular shi
Kunkurun ka san wanene. Daga ganin kuma sifar shi (mataimakin) za ka
gane shi.

Wato dai abin da nake qoqarin in ce shi ne, ka ga a nan suna zana
mutum, amma da ka gani za ka gane cewa wane ake nufi, duk da sun yi
masa mummunar kama. Ko da sun kamanta shi da Alade ne ko Kare, in
dai wane suke nufi, da ka gani za ka gane cewa wannan wane ne. To
wannan shigen irin wannan kenan. Ka ga a nan ma Dan Adam yana yi, to
ballantana Allah Mahallici.
Allah Ta’ala yana iya yin Alade mummuna ko Jaba mummuna, amma
mutanen da suka san mutumin a duniya in suka hango shi za su ce wancan wane ne, in sun gan shi a gidan wuta. Za su ce wane ne ga shi
can amma an yi masa halittar Gursunu.
Da za a yi mutum a Aljanna shi kuma a yi shi mai kyau, a yi shi
kyakkyawan gaske. Ko yaya ya kasance a nan duniya (saboda muni), to
in ka gan shi za ka ce wane ne, amma yanzu ya zama kyakkyawa. Wato
Allah Ta’ala zai iya ba shi siffarsa ta duniya da kyakkyawar kama.

*©Mahadi tukur Almizan*
[TASIRIN DABI'U]

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post