Yan Majilisar Dinkin Quraishawa !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
Sakamakon muna cikin lokuta ne na cigaba da murnar Mauludin Manzon Allah (S.A.W.W)naga ya kamata na kawo mana sunayen mafiya tsananin qiyayya da kuma cutar da Manzo (S.A.W.), domin sanin tarihi na daga cikin darusan da tarukan maulidi ke koyar da mu.
Su dai wadannan sune 'yan majalisa da ake tattaunawa da su wajen daukar mataki na cutar da Manzon Allah (S.A.W.W)da kuma sahabbansa (R.A).
Ga dai sunayensu kamar haka:-
(1)- ABU JAHAL BN HASHIM
(2)- ABULAHABIN BN ABDULMUDALLIB
(3)- ASWADU BN ABDUYAGUSIN
(4)- HARISU BN QAISIN BN ADIYYIN
(5)- WALIDU BN MUGIRATA
(6)- UBAYYU BN KHALAFIN
(7)- ABU QAISIN BN FAKHIRIN BN MUGIRATA
(8)- AASIY BN WA'ILI
(9)- NADDARU BN HARISIN
(10)- MUNABAHIN BN HUJJAJIN
(11)- ZUHAIRU BN ABIY UMAYYATA
(12)- SA'IBU BN SAIFIYU BN AABIDEEN
(13)- ASWADU BN ASWADIN
(14)- AL'ASIY BN SA'IDU BN AASIY
(15)- AL'ASI BN HISHAAM
(16)- UKUBATU BN ABIY MI'AIDIN
(17)- ABUL ASWADI AL-HUZALIYA
(18)- ALHAKAMU BN ABIY AASIY
(19)- ADIYYU BN AL-HAMRA'A
(20)- UTUBATU BN RABEE'ATA
(21)- SHAIBATU BN RABEE'ATA
(22)- ABU SUFYAN BN HARBIN.
Wadannan mutane sune mafiya tsananin gaba da Manzon Allah (S.A.W.W)a sarari, kuma duk daga cikinsu babu wanda ya muslimta sai Abu Sufyan Bn Harbin.
Shima Abu Sufyan din ya muslumta bisa tilasci ba wai bisa son ransa ba. Ya muslimta ne don ganin anci garin Makkah da yaqi, kuma rashin muslimtarsa zai jawo masa qasqanci. Saboda haka yaga muslimtarsa za ta zama masa riga ta rufa masa asiri.
Hakan ta bayyana qarara cewa ba don Allah ya muslimta ba, dalili kuwa shine yana daga cikin wadanda ake basu zakkah don lallashin zukatansu.
Ko da lokacin mulkin Usman Bn Affan sai da Abu Sufyan ya tara danginsa na kusa yake tabbatar musu kamar haka;
‘’ TO, GA SHI MULKI YA DAWO HANNUNKU, SAI KU RIQA JUJJUYASHI A TSAKANIN KU KAMAR YADDA AKE JUYA QWALLO (daga wannan zuwa wannan). KUMA KU SHAIDA BABU WUTA BABU ALJANNAH.....‘’.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
08126385470
~ 30th November, 2019.