Mafi Qarancin Kyau A Aljanna Shi NE Kyawon Annabi Yusuf (as)


_Inji Jagoran gaskiya [sayyid zakzaky]

Aka ce mana kuma, duk wanda ya shiga Aljanna, to aqallan kyan da
yake da shi shi ne na kyan Annabi Yusuf (AS). 

(Annabi Yusuf) dinnan da matar Waziri ta tattara mata da suka zarge ta cewa ta nemi yaron gidanta. Ta ce "ai ku ba a jarabce ku da abin da aka jarabce ni da shi
bane." Sai ta tattara su ta shirya su a shimfidu, suna duban juna ta ba su
matasai suka dan kishingida. Ta ba su dan abin tabawa da wuqaqen da
za a yayyanka abin tabawan.

 Sai ta ce wa Yusuf ya fito. Da suka gan shi,
ba su san lokacin da suka dinga yayyanka hannuwansu ba, suna kallo.

Sai da ya wuce sannan suka ga hannuwansu da jini. Suna kallon kyau ne.
To wannan kyau ne da Allah ya yi wa Annabi Yusuf a nan duniya.

Aka ce to duk wanda ya shiga Aljanna, in ma akwai mummuna a
Aljanna, to yana da kyan Annabi Yusuf (AS) ne, mafi qarancin kyau
kenan, don ba mummuna a Aljanna. Wato mafi qarancin kyau a Aljanna
shi ne kyawun Annabi Yusuf (AS). Ka ga wato in da mummuna shi ne
wannan kenan. Kuma kowane mutum kyan sa ya wuce nan. Wannan shi ne mafi qaranci, wanda kuma suka yi gaba duk sun wuce wannan.
 To daidai kyawun mutum daidai kyawun dabi'unsa. Saboda matsayinka a
Aljanna da halittar da za a yi maka…�
*®Mahadi Tukur Almizan*
[TASIRIN DABI'U]

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post