Kuzo kuga Magajin Annabawa Na gaskiya...!!


Idan ka ji ana cewa wane magaji ne ga wani, to, ba wai ana nufin mai cin gadonsa ne a bayansa ba.

Magaji yana nufin wanda ya gaji mutum ne a aiki, kuma ya suffantu da siffofinsa. Wannan dalili yasa Annabi (S A W W) ke cewa;

" MALAMAI MAGADA ANNABAWA NE, MATUQAR BASU SHIGA DUNIYA SUN SAJE DA (miyagun) SHUGABANNI BA. IDAN KUWA SUKA SHIGA DUNIYA SUKA SAJE DA (miyagun) SHUGABANNI, TO, SUN CI AMANAR MANZANNI, KU NISANCE SU  ."

KARANTA WANNAN:- Ina Jagoran mu,kuma a wane hali yake ??


Wannan hadisi ya fassara mana magadan Annabawa ne na gaskiya wadanda suka dace mu miqa wilayarmu gare su. Duk malamin da ka ganshi ya rabi azzaluman mahukunta, to, maciya amanar Manzanni ne, kuma shine za kaga shugabanni na sonsa don bai qyamaci miyagun ayyukansu ba.

Siffar magajin Annabawa (A.S) ta biyu bayan siffantuwarsa dasu ita ce, za kaga irin cutar da Manzanni da akayi da kuma qaryata su su ma hakan ne ke faruwa dasu.

Allah (T) na cewa;

" HAQIQA AN QARYATA MANZANNI DAGA GABANINKA, SAI SU KAYI HAQURI AKAN ABINDA AKA QARYATA SU, KUMA AKA CUTAR DA SU, HAR TAIMAKONMU YA JE MUSU. KUMA BABU MAI CANZAWA/MUSANYAWA GA KALMOMIN ALLAH (na faruwar irin wadannan abubuwa ga mai kira a dawowa littafin Allah). KUMA LALLE NE (labarin irin wannan cutarwar da kuma taimakon Allah) YA ZO MAKA DAGA LABARIN MANZANNI +da suka zo ka fin kai) ."

     (AN'AM:34)

Pls, wa kaga ya siffantu da wannan aya in ka cire Sayyid Zakzaky (H)  ?

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        08126385470

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post